Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, ya ce za a gurfanar da Babachir Lawal kotu, dangane da rawar da ya taka wajen harkallar kwangilar cire ciyawa a kogin Yobe da wasu ayyuka a sansanonon masu gudun hijira.
Osinbajo ya fada jiya Lahadi cewa shugaba Buhari ne ya bayar da wannan umarnin cewa hukumomin yaki da cin hanci su shirya gurfanar da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya din kotu.
Shi ne Sakataren Gwamnatin Buhari daga 2015 har zuwa ranar 0 Ga Oktoba, 2017 da aka kore shi daga aiki.
An samu Babachir Lawal da satar kudade na ayyukan agajin gaggawa.
Haka kuma Osinbajo ya ce Buhari ya bada umarnin a gurfanar da tsohon Babban Daraktan Hukumar Leken Asiri ta NIA, Mista Oke.
Oke shi ne shugaban NIA a lokacin da aka gano wasu milyoyin daloli kimshe a dakin da ke cikin wani gida a unguwar Ikoyi, Lagos, tun cikin watan Afrilu, 2017.
Tun farko dai Majalisar Dattawa ce ta fara fallasa Babachir Lawal, amma Buhari ya ce bai yi wani laifi ba.
Sai da ta matsa lamba ne sannan Buhari ya amince ya kori Lawal bayan anshafe tsawon lokaci ana caccakar Buhari.
Duk da an kori Babachir Lawal daga gwamnati, bai daina kusantuwa da Buhari ba. Hasali ma ya na cikin tawagar kamfen din sa na yakin neman zaben 2019 da ake kai yanzu.