Sojojin Najeriya sun tare babbar hanyar shiga garin Maiduguri, babban birnin jihar Barno daga Damaturu, sakamakon hare-haren Boko Haram a kan hanyar a cikin sa’o’i 48 da suka gabata.
Ba a dai san sai zuwa yaushe za su bude hanyar ba, amma dai yau Laraba da safe, an rika maida duk motar da ta nemi shiga Maidugurin inda ta fito.
Ana shiga Maiduguri ta hanyoyi shida ne, amma tun cikin 2014 aka datse sauran hanyoyi biyar din ba a bi ko shigowa birnin ta can, sai ta hanyar Damaturu kadai.
A can baya Boko Haram sun karya gadojin da ke hanyar bi a shiga Maiduguri, sai na kan hanyar Damaturu zuwa cikin Maiduguri ne kadai ba su samu nasarar karya ba.
Tun cikin 2014 sojoji da ‘yan sanda ke ta fama da Boko Haram, su na kokarin hana su karya Gadar Benishek, wadda ita kadai ce gada a tsakanin tafiyar kilomita 135, daga Damaturu zuwa Maiduguri.
A can baya da kuma kwanan nan bayan Kirsimiti, Boko Haram sun kai hare-hare a kan hanyar.
Sojoji da jama’a na tsoron idan Boko Haram suka karya Gadar Benishek, to za su cinye Maiduguri, domin babu wata hanyar da za iya shiga garin kenan.
Duk da cewa ba a bayar da dalilin rufe hanyar Maiduguri zuwa Damaturu ba, PREMIUM TIMES ta samu labarin cewa an kai hare-hare a kauyukan Ngamdu, da ke kan iyakar Yobe da Barno a jiya da dare.
A yau din nan wata majiyar sojoji ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa an ma hana motoci bi hanyar Damaturu din ita kan ta tun daga Pataskum a jihar Yobe.
Wato tun daga Pataskum har zuwa Maiduguri an hana motoci bi kenan, tafiyar kilomita 235 daga Pataskum zuwa Maiduguri.
Wani direban Vectra mai suna Ali, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa mun ma daina lodin fasinja, saboda sojoji sun rufe hanyar.
Shi ma wani dan kasuwa mai suna Sa’idu Baffa daga Damagun, kilomita 68 zuwa Damaturu, ya tabbatar wa PREMIUM TIMES da labarin datse hanyar tun daga karfe shida na safiyar yau Laraba.