RIGAKAFI: Gidauniyyar Bill da Melinda Gates za ta tallafa wa Najeriya da dala miliyan 75

0

A taron shirin tallafa wa jihohin da suka nuna himma wajen inganta fannin kiwon lafiyar su gidauniyyar Bill da Melinda Gates za ta tallafa wa fannin kiwon lafiyar Najeriya da dala miliyan 75.

Shirin mai taken ‘National Strategic Health Development Plan’ shiri ne da gwamnati ta shirya domin cimma burin samar da kiwon lafiya mai nagarta ga mutanen Najeriya.

Shirin zai tallafa wa fannin kiwon lafiyar jihohin da suka nuna himma wajen inganta fannin kiwon lafiyar su domin karfafa musu guiwowi.

Jam’in gidauniyyar Paul Bassainga ya sanar da haka a taron da aka yi a Abuja ranar Talata.

Bassainga ya jinjina wa kokarin da gwamnatin Najeriya ta yi a bangaren yin allurar rigakafi inda hakan ya sa gidauniyar za ta bata wannan tallafawa

” Ci gaban da Najeriya ta samu a fannin yin allurar rigakafi ya nuna cewa inganta cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na da mahimmanci ganin cewa sune suak fikusa da mutane.

” Sai dai matsalolin rashin kudade, rashin ma’aikata, rashin ingantattun kayan aiki na cikin matsalolin dake hana wannan kasar samar da kiwon lafiya mai nagarta.

A dalilin haka Bassainga ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta kara mai da hakali wajen ganin ta inganta cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko.

Idan ba a manta ba gidauniyyar Bill da Melinda Gates ta amince ta biya wa Najeriya bashin dala miliyan 76 da ta ciyo daga kasar Japan.

Najeriya ta karbo bashin ne don yin amfani da shi wajen ci gaba da yaki da cutar shan-inna da ta keyi.

Share.

game da Author