An gano cewa tsohon mataimakin jam’iyyar PDP, Babayo Gamawa, wanda jam’iyyar ta kora, shi kuma ya koma APC, Akwai zargin rarumar kudade har naira miliyan 500 a kan sa.
EFCC na binciken salwantar kudaden a hannun sa ba tun yau ba, kuma har ma an gurfanar da shi a kotu.
Ana zargin Gamawa ne tare da wasu mutane biyar a Bauchi da zargin karbar naira miliyan 500 na kudin kamfen a cikin 2015 lokacin ya na PDP.
EFCC ta ce kudaden na daga cikin makudan kudaden da tsohuwar ministan man fetur Diezani Allison-Madueke ta rika rabawa domin kamfen din 2015.
EFCC ta gurfanar da Gamawa a Babbar Kotun Tarayya da ke Bauchi, a cikin watan Yuni, 2018.
Amma dai PREMIUM TIMES ba za ta ce ga inda shari’ar ta tsaya a zuwa yanzu ba.
Gamawa ya koma jam’iyyar APC jiya Talata, bayan PDP ta dakatar da shi, bayan an yi masa zargin rashin gudanar da aikin sa, da kuma yi wa PDP zagon-kasa.
Gwamnan Jihar Bauchi, Abubakar Mohammed ne ya kai shi wurin Shugaba Muhammadu Buhari, wanda ya i murna sosai da komawar da ya yi cikin APC, jam’iyyar Buhari mai yaki da cin hanci da rashawa.
Da dama na ganin cewa goya Gamawa da Buhari ya yi, tamkar abin da Hausawa ke kira tsaftar biri ne, wai kashi a cikin moda.
Discussion about this post