Jam’iyyar ACPN wadda Oby Ezekwesili ta fara tsayawa takarar shugabancin kasa kafin ta bayyana janyewar ta daga takarar a yau Alhamis da safe, ta ce Shugaba Muhammadu Buhari za ta zaba a matsayin dan katarar shugaban kasa na APC.
Jam’iyyar ta kuma zargi Oby da kulla wata yarjejenya da wata jam’iyya cewa za a ba ta mukamin inista idan waccan jam’iyyar ta yi nasara.
Akwai kuma zargin ta da suka yi da karbar dala 5,000 da kuwa naira milyan 35 a matsayin gudummawa daga wasu jama’a.
Sun nemi ta kawo kayan jam’iyyar ta su ta ACPN da ke hannun ta.
Idan ba a manta ba a cikin wata sanarwa da Oby ta watsa a shafin ta na twitter a safiyar yau Alhamis, ta ce ta janye daga takarar ne domin ta gina gagarimar gamayyar wayar wa jama’a kai ta yadda za a guji jam’iyyu biyu din nan masu karfi, wato APC da PDP a lokacin zabe, har a kayar da su.
Oby ta ce ta yi tunanin daukar wannan mataki ne biyo bayan abubuwan da suka wakana yayin makabalar da yi tare da wasu ’yan takarar shugabancin kasa a makon da ya gabata.
Ta ce akwai bukatar a wayar wa ‘yan Najeriya kai cewa ba fa za a iya ci gaba ba, har sai an kawar da gungun ‘yan jam’iyyar APC da PDP.
Kakakin yada labarai na Oby, mai suna Ozioma Ubabukoh, ya tabbatar da janyewar da Oby ta yi.