Morata ya koma Atletico Madrid, De Jong Barcelona, Higuain Chelsea

0

Dan wasan Chelsea kuma tsohon dan wasan Real Madrid, Alvaro Morata, ya koma kungiyar Atletico Madrid da ke Spain.

A yau ne likitocin Atletico za su yi wa dan wasan gwaje-gwaje da aune-aunen tantace lafiya da kwarin jikin sa, ta yadda za a tantance ko akwai sauran wasu raunuka a jikin sa da kuma irin karfin kazar-kazar din sa a filin kwallo.

Kafar yada labarai ta Goal ta ce a yau Alhamis Morata zai bar Landon ya tafi Madrid inda zai koma buga gasar La Liga a kan kudi dala milyan 57.

Ita kuma Chelsea ta sayi dan wasan Argentina da ke buga wasa a Napoli wato Gonzalo Higuain.

Za ta saye shi a matsayin lamuni ne daga kungiyar Juventus, wadda ta bayar da shi lamuni ga Napoli.

Bayan nan, ita Kungiyar Barcelona ta sayi De Jong na kungiyar Ajax kan Yuro miliyan 85.

Dan wasan kwallon kafa na Najeriya, Mikel Obi da ya koma kasar China daga Chelsea, shima ya dawo kasar Ingila, inda zai murza tamolar sa a kungiyar kwallon kafa ta Middlesbourogh.

Share.

game da Author