Magidanci ya saki matar sa saboda ta rantse sai ta zabi Buhari

0

Wani magidanci a karamar hukumar Kanam, jihar Filato ya saki matarsa a dalilin rikici da ya kaure a tsakanin su saboda matar tasa ta rantse sai ta zabi Buhari.

Maigidan na ta ya ce matarsa ta tabbatar masa cewa ita fa Atiku za ta zaba a Faburairu.

Daga nan ne fa suka fara cacan baki a tsakanin su, shiko gogan naka sai ya mike tsaye ya falla mata mari. Ita kuma ta rika ce masa wallahi sai ta zabi Buhari.

Makwabta suka kawo dauki, daga nan sai ta arce da zuwa gidan su. Mahaifin ta ya nemi maigidanta ya zo domin a sasanta su.

Da ya zo sai ya karanta wa mahaifinta abinda ya hada su.

” Na yi ta nuna wa mata ta irin kwafsawan da Buhari yayi da irin bakin talaucin da ya saka mutanen Najeriya, cewa dole ne ta dawo daga rakiyar Buhari daga yanzu ta yi shirin zaben Atiku ko taki ko ta so, Amma tace atitir, ita Buhari za ta zaba. Daga nan ne fa muka kaure da rikici.

Bayan ya gama bayanin sa ne ita kuma ta ce Buhari ne zata zaba ba Atiku ba.

Shi kuwa maigidan na ta a gaban mahaifin ta ya dankara mata saki ya yi tafiyar sa abin shi.

Kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito Yan uwan matan sun nemi su yi masa dukan tsiya amma mahaifin su ya hana su.

Share.

game da Author