Za mu gudanar da sahihin zabe a 2019 -Shugaban INEC

0

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta Kasa, INEC, ya sake jaddada cewa hukumar sa za ta gudanar da sahihin zabe kuma ingantacce karbabbbe a 2019.

Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke jawabi a gaban mahalarta Taron Majalisar Sarakunan Gargajiya na Arewacin Najeriya, na 5 da aka gudanar ranar Laraba a Kaduna.

Yakubu ya ce ‘yan siyasar mu ba masu kishin dimokradiyya ba ne, dalili kenan suke yawan tsilla-tsillar canjin jam’iyya daga wannan zuwa waccan a kullum.

Ya ce INEC za ta kara inganta shirye-shiryen ta, ta yadda za ta tabbatar cewa an gudanar da zabe salum-alum ba tare da samun cikas ba a zaben 2019.

Daga nan ya kara da cewa gudanar da zabe a jiha daya tal ya fi wahala bisa ga gudanar da zabe na kasa a lokaci daya.

Ya ce gudanar da zaben kasa baki daya a kowace jiha a rana daya ya na da sauki fiye da a gudanar da zabe daya a wata jiha daya, domin idon jama’ar kasa gaba daya da hankulan su, zai karkata ne a kan waccan jihar da ake gudanar da zaben ita kadai.

Ya yi alkawarin cewa zaben 2019 zai kai gejin da duk kasashen duniya za su rika misali da shi wajen inganci da sahihanci.

Share.

game da Author