KASAFIN 2019: Dalilin da ya sa mu ka yi wa Buhari ihu a Majalisa

0

Daya daga cikin ‘Yan Majalisar da suka rika yi wa Shugaba Muhammadu Buhari sowa da eho jiya Laraba a Majalisar tarayya, ya bayyana PREMIUM TIMES dalilin sun a tozarta Buhari, a lokacin da ya ke gabatar da jawabin kasafin kudi na 2019.

Kinsley Chinda, dan Majaliasa daga jihar Rivers, ya bayyana cewa sun gwasale Buhari ne saboda yawancin maganganun da ya ke shaida wa ‘yan Najeriya dangane da halin da kasar nan ke ciki, ba gaskiya ba ne.

Ya ce kalaman na sa cike suke da tufka da warwara, musamman idan aka zo batun yin aiki da kasafin kudi.

“Shugaban Kasa ba ya yi mana adalci musamman wajen aiwatar da kasafinn kudi. A duk lokacin da ya kwafsa ko ya kasa gudanar da wasu abubuwa, sai ya dora laifin a kan mu ‘yan majalisa.

“Ka ga dai ya kasa gudanar da manyan ayyuka, wanda ya sa ba a yi wasu abubuwan da suka wajaba daga cikin kasafin 2018 masu yawa da muhimmanci ba.

“To mutumin da ya kasa gudanar da muhimman abubuwa, kuma shi da kan sa ya furta haka, ya kuma zai zo ya rika ba mu labarin wai ya inganta tattalin arzikin kasa mu kuma mu yarda?

“Shi da kan sa ya ce akwai ayyukan da aka yi kirdadon gudanarwa na naira tiriliyan 6.4, amma hakan bai yiwu ba, sai aka mirgina ayyukan a cikin kasafin 2019, maimakon a yi su cikin na 2018. To ka ga kenan kashi 16 bisa 100 kadai aka gudanar kenan.’’

Dan majalisar ya kara da cewa a lokacin da suke kewayen gani da ido a hukumomi daban-daban, sun kuma gano cewa da yawan hukumomin ba a sakar musu mafi akasarin kudaden da ya kamata a sakar musu kamar yadda shi Buhari ya rubuta zai yi a cikin kasafin 2018 ba.

Ya kuma yi tsokaci a kan yadda gwamnatin tarayya ke yin biris da dokokin kasa wajen aiwatar da wani abu, da kuma kin bin umarnin kotu.

A karshe ya ce ba ‘yan PDP kadai ba ne suka yi sowa da eho, har da ‘yan APC.

Share.

game da Author