Shin ko ka san Mata sun fi Maza yawan fama da ciwon kai?
A wani bincike da Kamfanin ‘Mintel’ dake kasar Britaniya ta yi bisa sanin ko tsakanin mata da maza wanne suka fi yawan fama da matsanincin ciwon kai.
Sakamakon binciken ya nuna cewa mata sun fi maza yin amfani da magungunan ciwon kai, da hakan ya nuna cewa sun fi maza yawan kamuwa da matsanancin ciwon ka. Sannan binciken ya gano haka ne bayan yin nazarin yawan jinsin mutanen da suka bukaci sannan suka sayi magungunan ciwon kai a kasar Britaniya.
Binciken ya nuna cewa a tsakanin watanni shida kashi 73 bisa 100 na mata ne suka sayi maganin ciwon kai cikin wadanda aka siyar a wannan lokaci.
Sannan kuma cikin wadannan kashi 73 bisa 100 da suka siya maganin akalla kashi biyar bisa 100 ne kawai suka iya daure wa na dan wani lokaci. Duk a wannan bincike, kashi 15 bisa 100 ne kacal na maza suka nemi magani na ciwon kai.
A bayanan binciken, shi wannan matsala na ciwon kai ya fi gallabar mata masu tasowa ne da wadanda suka yi aure. Kuma babban dalilin da ya sa suka fi fadawa cikin wannan matsala shine saka kan su cikin damuwa da suke yi.
A lokacin da mace ke tasowa, matsaloli irin na talauci da kuma hidindimun rayuwa kan zamo babban dalilin da kan sa kan mace ya buga tayi ta fama da ciwon kai.
Matsalar gidan aure da tunane-tunane na gida da al’amurran yau da kullum sannan da saka kai cikin damuwa duk suna daga cikin matsalolin dake sa mace ta fada cikin wannan matsala.
Wasu daga cikin shawarwarin da masu binciken suka bada ga mata shine su nisanta kan su daga yawan tunane tunane da sa kai cikin damuwa.
Sun ba da shawara musamman ga mata masu tasowa da su bi rayuwa cikin sauki sannan su kula da lafiyar su domin kauce wa fadawa cikin ababen da zai iya rikita musu lissafi su kasance cikin matukar damuwar da zai sa su rika samun yawan ciwon kai, a lokaci- lokaci.
Discussion about this post