Sarakunan Zamfara sun nemi a ba su bindigogi su tunkari maharan jihar

0

Sarakunan Jihar Zamfara sun yi kira da a ba su iznin mallakar bindigogi domin su tunkari maharan da suka addabi jihar da kashe-kashe da garkuuwa da jama’a tsawon shekaru da dama.

Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Zamfara, kuma Sarkin Anka, Mai Martaba Attahiru Ahmad ne ya yi wannan roki jiya Talata a Gusau, yayin da ake raba Babura ga zaratan sa-kai na yaki da mahara, wato CJTF da aka kafa kwanan nan a jihar.

An raba wa matasan sintirin hadin-guiwa din su 8,500 baburan hawa kowanen su.

“Karfin da kawai wadannan mahara ke da shi a kan mu, shi ne don su na rike da bindigogi samfurin AK 47 da suke rike. Alhali mu kuma ba ma dauke da komai, sai fa a wasu lokuta mu rike sanduna a matsayin amkamin kare kan mu.

Ya ce ya na da yakinin cewa idan sarakunan gargajiya, masu rike da mukaman siyasa da ma’aikatan gwamnati suka hada karfi, to za su iya yin galaba a kan maharan da suka mamaye jihar.

Ya roki gwamnati ta bayar da bindigogi samfurin AK47 kuma ta bayar da lasisin mallakar bindiga.

Share.

game da Author