Tsohon Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Imo, kuma sirikin gwamna Rochas Okorocha, ya fice dagac jam’iyyar APC ya koma AA, da a Turance ake kira Action Allience.
Uche Nwosu zai tsaya takarar gwamna a karkashin jam’iyyar AA ne bayan APC ta yi masa ta-leko-ta-koma kan neman zama dan takarar gwamna a karkashin jam’iyyar da ya yi, amma bai samu ba.
Ya bayyana wa manema labarai a filin jirgin saman Owerri jiya Talata cewa jam’iyyar APC din ce ta tilasta ya fice daga jam’iyyar.
“Jam’iyyar APC ta nuna rashin adalci karara a zaben fidda gwani, kuma ta nuna karfa-karfa a fii tare da rashin bin dokokin jam’iyya.”
Jam’iyyar APC ta afka cikin rikici a jihar Imo bayan da gwamna Rochas Okorocha ya kafe lallai sai sirikin sa Nwosu ne zai tsaya takarar gwamna a karkashin APC.
Wannan ne kuma ya hada Okorocha kakkausan fada da sa-in-sa tsakanin sa da shugaban jam’iyyar su, Adams Oshiomhole.
Ya kara da cewa duk wasu ‘yan APC a jihar Imo sun koma jam’iyyar AA, sai fa wadanda ke goyon bayan takarar sanata da gwamna Okorocha ya fito, su kadai ne suka rage a cikin jam’iyyar.
Ya ce komawar sa AA ba za ta hana masa goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari a zaben shugaban kasa ba.
Discussion about this post