A ranar Talata ne gwamnan jihar Bayelsa Seriake Dickson ya bayyana cewa zai jagoranci yaki da jabun magunguna a jihar.
Ya fadi haka ne a filin bajekolin magunguna da ake yi a jihar na Bayelsa
Dickson ya ce domin inganta yaki da jabun magunguna ne ya sa ya gina cibiyar tanttance magunguna a jihar.
” Daga yanzu duk asibitoci da shagungunan siyar da magunguna dake jihar za su rika karban magungunan su ne daga wannan cibiya bayan an tantance su.
Dickson ya kuma kara da cewa babbar burin sa shine ya ga ya inganta fannin kiwon lafiyar jihar yadda mutanen a Najeriya da na kasashen waje za su iya zuwa jihar domin samun biyan bukatun su na kiwon lafiya.
” Gwamnati ta dauki matakin ware kudade domin inganta fannin kiwon lafiyar jihar musamman fannin inshorar kiwon lafiya domin tabbatar cewa mutanen jihar sun sami ingantacciyar kulan da ya kamace su.
A karshe Dickson ya yi kira ga mutane da su yi koyi da abinda tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi na ‘sai an gwada ake sanin na kwarai’.
” Ina kira ga duk mutanen kasar nan da su zo su duba yadda muka inganta fannin kiwon lafiyar mu domin samun biyan bukatun su na kiwon lafiya.”