Dan takarar shugaban Kasa Atiku Abubakar ya bayyana wa dubban ‘yan Jam’iyyar PDP a garin Sokoto cewa shi fa mutum ne da komai da ruwan ka.
Atiku da jiga-jigan Jam’iyyar PDP sun isa garin Sokoto ne domin kaddamar da kamfen din shugaban kasa da jam’iyyar ta gudanar a garin na Sokoto.
A jawabin da ya yi, Atiku ta ce kakannin sa daga garin garin Wurno suke, Kuma shi cikakken bafulatani ne.
” Ina kira gare ku duka da kada ku sake sauraren wadanda zasu ce muku suna da Shanu 150 a tsawon shekaru da dama. Ni shanu na sun fi dubu.
” Ni cikakken dan kasuwa ne mai komai da ruwan ka. Ni hamshakin manomi ne, sannan kuma dan kasuwa, kuma ni ma’aikacin gwamnati ne da a dalilin haka ya sa na fi duk wani dan takara cancanta ya mulki kasar nan ko don inganta halin matasan Najeriya suka fada na matsi da rashin aiki.
Ya kara da cewa a zaben 2019, zabe ne da za ayi ba wai don komai ba sai don a kau da yunwa da talauci da yayi wa mutane katutu, sannan kuma da samar da tsaro da aikin yi ga matasa.
A wajen wannan taro, shugaban jam’iyyar PDP, Uche Secondus ya mika wa ‘yan takarar gwamna na yankin Arewa maso Yammacin Najeriya tuta.
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, Namadi Sambo, Bukola Saraki, Yakubu Dogara, Rabiu Kwankwaso, Sule Lamido da sauran jiga-jigan ‘yan jam’iyyar sun halarci wannan taro.