A ranar Lahadi ne shugaban hukumar(NAFDAC) Moji Adeyeye ta bayyana cewa hukumar za ta kona kayan da ta kama da ya kai na Naira biliyan 198.
Adeyeye ta fadi haka ne a taron bukin cikan ta shekara daya da darewa shugabancin hukumar a Abuja.
Ta bayyana cewa cikin kayan da hukumar za ta kona sun hada da kwantinonin kwayoyin Tramado.
” Mun kuma kama kwantina 25 dankare da kwayoyin Tramadol da ya kai na Naira biliyan 1.7 kuma mun gurfanar da mutane uku da ke da hannu a harkar shigo da kwayoyin.
Bayan haka Adeyeye ta bayyana cewa a shekara daya hukumar ta biyan dukkan basukan da gwamnati ke binta da ya kai Naira biliyan 3.2.
Discussion about this post