Amina Mohammed wata mata ce da ta shiga hannu bayan yin amfani da damar da ta samu na iya shiga kurdi-kurdi, sako-sako na musamman sashen uwargidan shugaban Kasa ta na damfarar ‘yan Kasuwa da gaggan ‘yan siyasa a matsayin ita yar cikin gida ne.
Rundunar tsaro na sirri, wato SSS ta cafke Amina Mohammed ne bayan an kama ta da laifin yin amfani da takardun ofishin Uwargidan shugaban kasa ta na yin damfara da su.
Bincike ya nuna cewa akwai lokacin da ta taba yi wa wasu karya a fadar shugaban kasa cewa ita matar gwamnan jihar Kogi ce, Yahaya Bello.
Asirin Amina ya tonu ne bayan ta damfarar wani hamshakin dan kasuwa kudi har naira Miliyan 150 wai zata yi masa hanya a bashi tafkeken fili da gwamnati ke siyarwa.
Bayan nan kakakin hukumar SSS Peter Afunanya ya bayyana cewa hukumar ta kama Amina da laifin satan sunayayen manyan ma’aikatan fadar gwamnati tana damfara mutane makudan kudade.
Afunanya ya bayyana cewa cikin sunayen da Amina ta kan yi amfani dasu wajen damfarar mutana a fadar shugaban kasa sun hada da Justina Oluha sannan akan kira ta Amina Villa.
A haka ne ta damfari wani Alexander Chicason Naira miliyan 150 wai za ta yi masa hanya ya samu fili da gwamnati ke siyarwa.
” A haka ne fa Chicason ya bata cin hancin wadannan miliyoyin naira ganin kusancin ta da fadar gwamnati.
Bayan haka Amina ta bayyana cewa ta aikata haka ne da taimakon wata ‘yar uwan mai dakin shugaban kasa mai suna Moriyatu da kuma tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal.
A yanzu dai Amina ta na rokon ‘yan Najeriya da su saka baki akan abinda jami’an tsaro ke yi mata cewa kada su bari a ci gaba da tare ta da yi mata wulakanci ganin dai shi wannan harka har da ‘yar uwar Aisha Buhari wato Moriyatu suke aikatawa.
Amina ta kara da cewa sai da tayi watanni 4 a tsare kuma yanzu haka ma shirin ci gaba da tsare ta ne SSS din suke kokarin yi.
Amma sai dai Afunanya ya karyawatan Nuwamba ta kawo kanta ofishin SSS din
A karshe Afunanya da maitaimaka wa Aisha kan harkokin yada labarai Sulaiman Haruna sun ce basu da tabbacin ko ‘yar uwan Aisha Buhari wato Moriyatu na cikin wadanda suka aikata wadannan laifi kamar yadda Amina ta fadi.
Sai dai ana nan ana ci gaba da bincike akai.
Discussion about this post