Duk da zanga-zangar ma’aikatan majalisar kasa, Buhari zai gabatar da kasafin 2019 ranar Laraba

0

Duk da Zanga-Zangar da ma’aikatan majalisar kasa da yasa mutane basu iya shiga ko gudanar da hidindimun sa a a majalisar, Shugabannin majalisar sun bayyana cewa za a karbi bakuncin shugaban kasa Muhammadu Buhari domin gabatar da kasafin kudin 2019 ranar Laraba.

Majalisar ta amince da haka ne a yau Talata bayan shugaban masu rinjaye na majalisar tarayya Femi Gbajabiamila ya jagoranci mahawara game da haka a zauren ta.

A mahawara, majalisar ta amince ta dakatar da dokokin majalisar domin Buhari ya bayyana a gaban ta domin gabatar da kasafin kudin kasa Najeriya ta 2019.

Idan ba a manta ba a ranar Larabar da ta gabata ne Buhari ya rubuta wa majalisa wasikar cewa zai bayyana ranar Laraba domin gabatar da kasafin kudin 2019.

Share.

game da Author