2019: Ba mu bayyana wanda kungiyar mu za ta zaba ba tsakanin Buhari da Atiku – Miyetti Allah

0

Kungiyar makiyaya na Miyetti Allah ta bayyana cewa babu dan takarar da take marawa baya a tsakanin Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar a zabe mai zuwa.

Shugaban kungiyar Bello Badejo ya sanar da haka yayin da ya ziyarci gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal ranar Talata.

Badejo ya bayyana cewa duk da cewa Buhari da Atiku Fulani ne amma har yanzu babu takamamman tsarin bunkasa aiyukkan makiyayan da suka yi a kasar nan ba.

Ya ce gwamnatin Buhari ta kafa bankunan da za su rika tallafa wa manoma da basussuka da kayan aiki amma makiyaya kuwa shuru kake ji.

Bayan haka Badejo ya kuma koka game da yadda wannan gwamnatin ta yi watsi da al’amuran kawar da rikicin dake tsakanin makiyaya da manoma a kasar nan.

Ya ce gwamnati ta fito da shirin kebe filaye domin makiyaya su sami wurin kiwon dabobbin su a killace amma sai dai wasu jihohin ne suka fara amfani da shirin maimakon kasa baki daya.

Badejo yace samar da dawwamammen hanyar sassanta rikicin dake tsakanin makiyaya da manoma zai taimaka wajen samar da zaman lafiya a kasar nan.

A karshe ya ga laifin yadda gidajen jaridu ke yada labaran ricikin dake tsakanin makiyaya da manoma inda ya ke cewa mafi yawan gidajen yada labarai basu sauraron bangaren makiyaya kafin su yada labaran su.

Share.

game da Author