Tsohon shugaban kasa Abdussalami Abubakar ya karyata wasu daga cikin ‘yan takara da suka ki halartar taron saka hannu na yarjejeniya zaman lafiya da aka yi a Abuja cewa wai ba a gayyace su ba.
Dan takarar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana cewa dalilin da ya sa bai halarci wannan taro ba shine don ba a gayyace si ba.
Idan ba a mata ba a yau Talata ne kungiyar hadin kai da zaman lafiya wanda tsohon shugaban Kasa Abdussalami Abubakar ke jagoranta ta shirya taron saka hannu a yarjejeniyar zaman lafiya ga jam’iyyun kasar nan.
Shi dai irin wannan yarjejeniya akan yi shi ne idan zabe ya tunkaro inda gaggan ‘yan takara kan hadu wuri daya su rattaba hannu a wannan takarda da fatan a yi zabe lafiya.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya halarci wannan taro kuma ya rattaba hannu a wannan yarjejeniya.
Sai dai kuma babban abokin hamayyar sa kuma dan takarar shgabancin kasa a jam’iyyar PDP Atiku Abubakar bai halarci wannan taro ba.
Da muka ne mi ji daga bakin kakakin sa, Ya ce Atiku bashi da masaniyar wannan taro da aka yi da karfe uku na rana.
“I na tabbatar muku cewa Atiku Abubakar bai samu gayyata zuwa taron ba.” Haka Kakakin yada Labaran sa, Paul Ibe ya shaida wa Premium Times, a cikin wata sananrwa da ya fitar.
Karanta hirar da PREMIUM TIMES ta yi da Abdussalami bisa wannan korafi na wasu ‘yan takara.
TAMBAYA: Atiku ya ce ba a gayyace shi ba. Ina dalili?
ABDULSALAMI: To ka dai ga yawan jam’iyyun da suka halarci taron yarjejeniyar. Wannan kuma shi ne zai iya bada amsar dalilin rashin zuwan na sa ba ni ba. Mu kuwa wane dalili gare mu da za mu ki gayyatar kowa? Wannan sanya hannu kan yarjejeniya ta dukkan jam’iyyun siyasa ce, da nufin amincewa a yi da’a da biyayya ga tsarin da dokoki suka gindaya a lokacin zabe.
To amma idan ma har akwai miskilar rashinn isar sakon wasikun gayyata ga wasu, ni dai ban sani ba.
TAMBAYA: Ka na ganin rashin zuwan Atiku zai iya rage wa yarjejeniyar karfi da karsashi?
ABUBAKAR; Ta yaya rashin zuwan mutum daya zai iya rage wa yarjejeniyar da mutane da yawa suka kulla karsashi? Ba na jin zai rage mata karfi ko karsashi.
TAMBAYA: Amma ba ka damu ba ganin cewa banda Atiku har da irin su Ezekesili, Donald Duke da sauran su duk ba su halarta halarta ba. Abin ya nuna kamar shugaban kasa ne ya yi wa taron yarjejeniyar banga-banga.
ABUBAKAR: Wato kai ka na zargin cewa mu na yi wa shugaban kasa aiki ne kenan ko?
TAMBAYA: A’a, ban zarge ku ba.
ABUBAKAR: To tunda ba argin mu ka ke yi ba, mu dai abin da muka sani, babu wani dan takarar shugaban kasa ko jam’iyyar da ba mu gayyata ba. Kuma ka dai ga yawan jama’ar da suka halarta da idon ka.
TAMBAYA: To ko akwai yiwuwar wadanda ba su halarci taron na yau ba, daga baya su zo su rattaba hannun amincewar ta su?
ABUBAKAR: Kwarai kuwa, kofa a bude ta ke, duk wanda bai zo ba, zai iya zuwa daga baya a rattaba hannun amincewa.