Dan takarar jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa na 2019 mai zuwa, Atiku Abbakar, ya bayyana cewa bai halarci taron rattaba hannun yarjejeniyar tabbatar da zabe cikin kwanciyar hankali da lumana da aka gudanar yau Talata a Abuja ba, saboda ba a gayyace shi ba.
“I na tabbatar muku cewa Atiku Abubakar bai samu gayyata zuwa taron ba.” Haka Kakakin yada Labaran sa, Paul Ibe ya shaida wa Premium Times, a cikin wata sananrwa da ya fitar.
Ibe ya yi wannan karin haske ne jim kadan bayan da PREMIUM TIMES ta buga labarin cewa Atiku bai halarci taron ba, wanda a lokacin ya ke gudana a Babbar Cibiyar Taro ta ICC da ke Abuja.
Kwamitin Jaddada Zaman Lafiya, a karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Atiku Abubakar ne ke shugabantar kwamitin.
Wasu ‘yan takarar shugaban kasa da suka halarci taron, sun hada da Buhari. Amma irin su Kingsley Moghalu da Oby Ezekwesili duk ba su halarta ba.
Haka shi ma dan takarar AAC, Omoleye Sowore, shugaban jaridar Sahara Reporters, shi ma bai halarta ba.
Oby ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa ba ta samu takardar gayyata ba.
Sai dai kuma daya daga cikin jiga-jigan kwamitin, Mathew Hassan Kukah, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa tabbas sun gayyaci Atiku, domin sun aika masa da takardar gayyata.