Yara sama da 900,000 na fama da matsanancin yunwa a Arewacin Najeriya -UNICEF

0

Asusun bada tallafi ga kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ta koka kan yadda ake samun yawan yara da ke fama da matsanancin yunwa a yankin Arewa Maso Gabashin Kasar nan.

UNICEF ta fadi haka ne a taro da akayi a Jihar Adamawa.

Jami’ar asusun Bamidele Omotola ta bayyana cewa bincike ya nuna cewa sama da yara 900,000 na nan a jihohin dake arewa maso gabacin kasar nan kuma suna fama da matsinacin yunwa.

Ta ce hakan na da nassaba ne saboda aiyukkan Boko Haram da ya addabi mutanen yankin.

” Bincike ya nuna cewa matsalar yunwa yana ta yadu a sauran sassan Najeriya domin kuwa a yanzu haka yara miliyan 25 na fama da ciwon rama sannan miliyan 10 basa girma yadda ya kamata.

Idan ba manta ba a kwanakin baya ne ministan Tsare-tsare Udo-Udoma ya yi kira ga gwamnatocin jihohin kasar nan da su maida hankali wajen yakar matsalar yunwa da ake fama da shi musamman ga yara kanana.

Ya ce bincike ya nuna cewa yara miliyan 2.5 a Najeriya na fama da matsanancin yunwa sannan illar haka na kawo rauni ga kaifin kwakwalwar yara da hana su girma yadda ya kamata.

A karshe Udoma ya kara da cewa ma’aikatar sa ta bude wani asusu na musamman domin taimakawa yaran dake fama da yunwa a kasar nan. A haka kuma yake kira ga gwamnatoci da ma’aikatu da su bi sahun ma’aikatar tsare-tsare domin samun nasarar kau da wannan matsala a kasar nan.

Share.

game da Author