MALLAKAR KUDADEN JABU: Kotun Kano ta daure Malam Mairakumi shekara 10

0

Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta yanke hukuncin daurin shekara 10 a kurkuku, kan fitaccen malamin nan Abubakar Ishaq, wanda aka fi sani da Mairakumi.

An yanke wa Mairakumi wa’adin shekaru goma a gidan Yari ne, saboda an kama shi da takardun kudade na dalolin Amurka na jabu a cikin gidan sa.

Mai Shari’a Lewis Allagoa ya samu Mairakumi da laifuka biyu, wadanda a kan su ne aka yanke masa hukuncin daurin shekaru biyar a kowane laifi.

Hukumar NDLEA ce ta kama shi, kuma ita ce ta damka shi a hannun EFCC, ta gurfanar da shi kotu, makonni uku da suka gabata.

Mairakumi ya afka cikin markabu tun bayan da EFCC ta karbe shi daga Hukumar Hana Tu’ammali da Miyagun Kwayoyi, NDLEA, saboda a wani farmaki da ta kai gidan sa, an same shi da mallakar dalolin Amurka 176 kuma duk na jabu.

Daga nan ne aka gurfanar da shi a Babbar Kotun Tarayya, aka yanke masa hukunci bayan an same shi da laifi a tuhumomi biyu da ake yi masa.

Kafin sannan kuma, ya nemi a sasanta a kan tuhumomi na 3 da na 4, wanda mai gabatar da kara, lauyan mai gabatar da kara, Samuel Chime ya nemi kotu ta amince.

Sai dai kuma lauyan wanda ake kara, Mohammed Aliyu ya nemi kotu ta yi wa Mairakumi sassauci, inda mai shari’a ya kauda kai daga yin haka.

Amma kuma kotu ta ce mai laifin zai yi wa laifukan biyu zaman wa’adin su a kurkuku a lokaci daya. Watau Mairakumi zai shafe shekaru biyar ne a kurkuku ba goma ba.

Bayan an gama yanke hukunci, nan take Mai Shari’a ya bada umarnin a kone kudaden jabun da aka samu a gidan Mairakumi.

Share.

game da Author