Kotu ta daure wani da ya yi fasikanci da yaro ta dubura a Gombe

0

Kotu dake Tunfure jihar Gombe ta daure wani magidanci mai suna Zakariya Shehu da ta kama da laifin yin lalata da dan shekara 12 ta dubura.

Lauyan da ya shigar da karar Kabiru Shuaibu ya bayyana wa kotu cewa Shehu mai shekar 29, mazaunin kwatas din Jekadafari ne a garin Gombe sannan ya aikata wannan ta’asa ne a watan Satumba.

Ya ce Shehu ya danne wannan yaro ne a dakin ajiye kaya a Tashar Dukku dake garin Gombe .

Shuaibu ya nemi alfarmar kotun data daga shari’ar wannan kara domin jami’an tsaro su kammala bincike.

Alkalin kotun Japhet Maida ya daga shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Nuwamba sannan ya bada umurin a tsare Shehu a hannu ‘yan sanda har sai an kammala shari’ar.

Share.

game da Author