KARIN ALBASHI: A bar kowace jiha ta biya daidai nauyin aljihun ta – El-Rufai da Ahmed

0

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa kuskure ne a ce za a fito da tsarin karin albashi na bai-daya a kasar nan, ya na mai ra’ayin cewa a bar kowace jiha ta kayyade mafi kankantar albashin ma’aikatan ta daidai yadda za ta iya, kuma gwargwadon kudaden shigar da ta ke samu.

El-Rufai ya yi wannan jawabi ne a wurin wani taron Kungiyar Gwamnonin Arewa, a Abuja.

Daga nan kuma sai El-Rufai ya nemi a sake yi wa doka kwaskwarima domin a kyale kowace jiha ta biya daidai karfin aljihun ta kawai.

“Idan ku ka kalli dokar Najeriya ta 1963, babu ma zancen mafi kankantar albashi a cikin ta, an kakaba ta ne a lokacin mulkin sojoji.

“Don haka akwai dokoki da dama da aka shigo da su a cikin dokokin kasar nan a lokacin mulkin sojoji, wadanda ke da bukatar a sake duba su, domin a yi musu gyara da kwaskwarima.”

Gwamna El-Rufai ya buga misali da adadin kudaden shigar da jihar Kaduna ke samu.

Ya ce a cikin 2015 jihar Kaduna ta tara kudaden shigar da kuka kai naira bilyan 11, amma a cikin shekarar 2017 ta tara abin da ya haura naira bilyan 20.

Ya ce don haka a yi wa doka gyara, yadda kowace jiha za ta iya biyan albashi daidai iyawar ta, kuma daidai da adadin kudaden shigar da ta ke samu a kowane wata ko kuma kowace shekara.

Shi ma gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed, yay i karin haske da cewa wannan batun karin albashi fay a zo ne a daidai lokacin karinn samun kudaden shiga ba zai fara aiki ba tukunna.

Ya ce idan za a yi batun karin albashi, to akwai matukar bukatar yin daidaito tsakanin tattalin arziki da kuma ayyukan neman kudaden shiga domin kara samun kudaden da ke shigo wa jiha daga haraji da sauran tara da ake yanka wa kamfanoni, masana’antu, daga hukunci da sauran nau’ukan kudaden shiga.

Shi ma y ace dole sai an sake duba doka idan ana so a yi maganar karin mafi kankantar albashi, domin za a kara wa jihohi wani nauyi ne na biyan kudade sosai.

Shi ma ya buga misali da kudaden shigar da jihar Kwara ke Tarawa a duk shekara, wadanda ko kadan ba su ma kama kafar wadanda jihar Kaduna ke Tarawa a duka shekara ba.

Share.

game da Author