Kotun Daukaka Kara a Abuja, ta kwace karfin ikon Kwamitin Shugaban Kasa mai Kwato Kadarori da kuma ikon kwamitin na gurfanar da wadanda ake zargi kotu.
Masu Shari’a biyar ne suka yi zaman yanke hukunci a karkashin jagorancin Mai Shari’a Hussein Mukhtar, inda su biyar din suka yanke hukuncin cewa Kwamitin Shugaban Kasa ba shi da ikon tunkarar kotu a kan batun wani da ake zargi da mallakar kantama-kantaman kadarori domin su gurfanar da shi.
Wannan hukunci ya taso ne biyo bayan wata kara da wani ma’aikacin gwamnati mai suna Tijjani Tumsah ya shigar.
Tumsah, wanda ma’aikaci ne a Ma’aikatar Makamashi, Ayyuka da Gidaje, ya shigar da karar ce ta hannun lauyan sa mai suna Kehinde Ogunwumiju, wanda babban lauya ne mai mukamin SAN.
Ya shigar da karar ne bayan kwamitin ya kwace masa wasu kadarori kuma an shigar da shi kara kotu.
Lauyan ya tabbatar wa PREMIUM TIMES hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke, a lokacin da ake tattaunawa da shi ta wayar tarho, kuma ya aiko wa jaridar wani sashi na kwafen hukuncin da kotun ta yanke.
Ya ce kotu ta ce aikin kwamitin ba ya na nufin har da yin azarbabin kwace kadarorin jama’a ba ne, tun kafin shari’a ta tabbatar masa da laifi a kan sa.
Don haka kwamitin ba shi da hurumin kwace kadarori, kuma ba shi da ikon gurfanar da wadanda ake zargi a kotu.
Kotun ta ce bincike ne kawai aikin kwamitin, kuma a iyar bincike ya kamata ya tsaya.
Bayan kammala bincike, kotu ta shawarci kwamiti cewa wurin shugaban kasa za su rika mika rahoton binciken su, domin shi ya nada su.
Dama ko Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu, sai da ya maka kwamitin kara a kotu, ya na kalubalantar yadda kwamitin ke garzayawa kotu su na karbo sammacin kwace kadarori, kamar yadda aka yi masa a baya.