Wasu mahara sun gudu da daliban sakandare sama da 80 a birnin Bamenda, da ke yammacin kasar Kamaru.
Majiyar jami’an sojoji sun tabbatar da cewa an gudu da daliban ranar Lahadi.
Har ya zuwa jiya Litinin babu wata kungiyar ta’adda ko mahara da ta yi sanarwar hannun ta wajen yin garkuwa da daliban.
An sace daliban ne a cikin yankin Kamaru da ke magana da harshen Turancin Ingilishi, yankin da wasu ‘yan tawaye ke fadan neman ballewa daga kasar.
“An sace mutane 81, ciki har da shugaban makarantar. An tsere da su a cikin jeji.” Inji wata majiyar sojoji.
Rahotanni sun ce an sace dalibai 78, direba daya da kuma wani malami.
Kakakin Gwamnatin kasar ya ce hukuma na bin sawun maganar, amma ba gwamnati ba za ta yi hanzarin cewa komai ba a yanzu tukunna.
Wata jaridar Kamaru mai suna Journalducameroon.com, ta ce mahara sun yi wa sakandare ta Presbyterian Secondary School dirar mikiya, a Nkwem, sannan suka tattara daliban suka arce da su.
An sace su ne a lokacin da suke kokarin rubuta jarabawar fita sakandare ta GCE, inda bayan an gudu da su kuma, maharan suka nuno su a kafar yada labarai ta soshiyal midiya.
Hukumomin tsaro sun ce su na bakin kokarin ganin cewa sun gano su, kuma sun kubutar da su.