Tsohon Gwamnan Jihar Abia, Orji Kalu ya fice zuwa kasashen waje domin neman magani, duk kuwa da damka wa kotun tarayya takardun biza da fasfo da ya yi.
Hukumar EFCC ce ta yi wannan korafin jiya Litinin a kotu, a ta bakin lauyan hukumar, Rotimi Jacobs.
Jacobs ya ce EFCC ba ta da masaniyar kotu ta bai wa Kalu iznin ficewa daga waje, domin ba a sanar da hukumar ba.
An tsaida shari’ar da ke tuhumar Kalu da salwantar da naira bilyan 7.65 a kotun tarayya da ke Lagos, saboda a jiya din Kalu bai je kotun ba.
Lauyan EFCC Jacobs ya ce rashin halartar Kalu shiri ne kawai domin kawo wa shari’a tsaiko, kuma ficewar sa zuwa kasashen waje, ya karya sharuddan beli, ya arce waje kenan.
Ya ce ba su da masaniyar an ba Kalu izninn tafiya waje neman magani, sai kawai ta bakin kakakin yada labaran Kalu, Kunle Oyewunmi suka ji zancen.
Kafin sannan, lauyan Kalu, Awa Kalu, ya shaida wa kotu cewa Kalu ya fita kasar waje inda aka yi masa fida, kuma an ba shi shawara da ya zauna can har sai bayan ya wartsake tukunna.
Lauyan Kalu ya ce wanda ya ke karewar ya fice zuwa neman magani ne, bayan da kotu ta bada sanarwar dakatar da ci gaba da sauren shari’ar sa ha sai yadda hali ya yi.
Sai dai kuma Mai Shari’a Mohammed Idris ya bayyana cewa duk da dai kotu ta dage zaman a ranar 27 Ga Satumba, ta ce har sai yadda hali ya kama, to an aika wa Kalu sammacin ci gaba da shari’a a ranar 2 Ga Nuwamba.
Idris y ace tabbas kotu ta samu sako ta e-mail mai nuna cewa Kalu na shirin tafiya neman magani a waje, amma dai ba a hado wa kotun takardun shaidar irin ciwon da ke damun sa ba, ko tuma irin maganin da ya yi ta nema a nan Najeriya, kafin ya yanke shawarar ficewa waje.
A kan haka ne Mai Shari’a ya yanke hukuncin cewa daga ranar ba zai kara daga shari’ar ba, don haka ya umarci Kalu da ya dawo Najeriya a cikin kwanaki bakwai.
Za a ci gaba da sauraren karar a ranar 12 Ga Nuwamba, ranar da Mai Shari’a ya ce tilas sai Kalu ya gabatar da kan sa a gaban kotu.
Discussion about this post