Ministan yada labari, Lai Mohammed ya gargadi gwamnatin Amurka da su nesan ta kansu daga kokarin amincewa dan takarar shugabancin Najeriya a inuwar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar takardar Izinin Shiga kasar Amurka.
Lai ya bayyana cewa idan har aka yi haka to tabbas zai iya yin nuni kamar Amurkan tana mara masa baya na zaben 2019.
” Kasar Amurka na da Ikon mika wa duk wanda ta so takardar izinin shiga kasar ta amma abinda muke so su lura da shi shine a wannan lokaci bai dace ba domin idan suka yi haka zai nuna kamar su Amurka din ta amince da takarar Atiku ne kuma shi za ta mara wa baya a 2019.
” Muna sane cewa Atiku yayi hayan wasu kwararru domin su lallabi kasar Amurka ta yarda ta bashi wannan takarda. Ba za mu iya hanawa ba amma dai a yanzu idan suka yi haka zai nuna kamar ita Kasar tana mara wa Atiku baya ne.
Discussion about this post