Sanatocin da wakilai da ke wakiltar jihar Kano a majlisar Kasar sun bayyana goyon bayan su ga gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.
Wakilan sun bayyana haka ne a takarda da shugaban su sanata Kabiru Gaya ya saka wa hannu ranar Alhamis.
” Dukkan mu a majalisar Kasa mun gamsu da irin ayyukan ci gaba da gwamnan jihar Kano yayi tun daga hawan sa a 2015.
Muna tare da shi dari bisa dari.
Wakilan sun kara da cewa barazanar wani bidiyo da aka wallafa da ya nuna gwamna Ganduje ya na karkacewa yana zura daloli a aljihun babban rigar sa na cin hanci daga wajen dan kwangila bai dada su da kasa ba kuma ba zai sa su yi wa Ganduje bore ba.
” Wannan bidiyo ba zai sa mu yi wa gwamnan mu tawaye ba. Muna tare da shi kuma zamu yi masa aiki tukuru don ganin ya lashe zaben 2019 a Kano. Wannan bidiyo an sake sa ne kawai don a ci masa mutunci amma aikin da yake yi wa mutanen jihar Kano ya isa mu yi watsi da shi mu hada kai domin ci gaban jihar da gwamna Ganduje.
” Bayan nan muna rokon shugaba Muhammadu Buhari da ya toshe kunnuwar sa daga sauraren masu kitsa masa karerayi game da gwamna Ganduje, cewa dukkan su suna neman fada ne amma babu alkhairin dake tattare da irin wadannan mutane.
‘Yan majalisar tarayya 16 da suka saka hannu a wannan takarda sun hada da Abdulmumin Jibrin, Nassiru Ahmed, Tijjani Jobe, Alhassan Doguwa, Abdullahi Gaya, Badamasi Ayuba, Bashir Baballe, Munir Danagundi, Aminu Suleiman, Mustapha Dawaki, Sulaiman Aliyu Romo, Muhammad Wudil, Muktar Chiromawa da Sani Bala.
Discussion about this post