An nada Atiku wazirin Adamawa na 7 a fadar Lamido

0

Lamidon Adamawa mai martaba Mustapha Barkindo ya bayyana cewa gudunmuwar da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya yi wa jihar Adamawa da kasa Najeriya ba su misaltuwa.

Barkindo ya fadi haka ne da ya ke nada Atiku Abubakar Wazirin Adamawa na bakwai.

” Waziri ba gadon shi ake ba, kowa zai iya zama Waziri. In kira ga sauran sarakunan wannan jiha da su ba sabon waziri duk wani hadin kai davya ke bukata domin samun nasara a wannan sabon matsayi na sa.

Shima tsohon shugaban Kasa Olusegun Obasanjo kira yayi ga Waziri Atiku da ya maida hankali wajen hada kan al’umma.

Wakilin shugaban kasa Muhammadu Buhari kuma ministan Abuja, Musa Bello yi wa sabon Waziri fatan alkhairi a matsayin sakon shugaba Buhari.

Cikin wadanda suka halarci wannan buki sun hada da shugaban majalisar wakilai ta tarayya da na dattawa, Dogara Yakubu da Bukola Saraki.

Goodluck Jonathan da Namadi Sambo, sannan da gwamnonin Gombe, Sokoto,Bayelsa da Taraba duk sun halarci wannan buki.

Share.

game da Author