Gwamnatin tarayya ta yi kira ga gwamnatocin jihohi da su dage wajen wayar da kan mutane game da hadarin dake tattare da kamuwa da zazzabin Lassa.
Bincike ya nuna cewa a watanni 11 da suka gabata mutane 559 sun kamu da cutar a inda 143 daga ciki suka riga mu gidan gaskiya.
A dalilin haka ne ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya bayyana cewa wannan karon gwamnati ta fara shirin ganin cutar bata yadu a kasa ba ta hanyar fara shiru tun yanzu da kuma wayar wa mutane kai game da cutar da yadda za su kiyaye kan su.
” A yanzu haka mun horas da m’aikatan da za su wayar wa mutane kai musamman a yankunan karkara.
” Asibitocin mu na ajiye da magungunan kawar da wannan cuta na zazzabin Lassa.
A karshe hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta bayyana cewa za ta hada hannu da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) domin inganta ayyukan su game da cutar.