Buhari, El-Rufai sun aika da sakon ta’aziyyar su ga iyalan marigayi Abba Kyari

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aika da ta’aziyyar sa ga Iyalan marigayi Janar Abba Kyari.

Abba Kyari ya rasu yana da shekaru 80 sannan ana sa ran za a yi jana’izar sa da misalin karfe 4 na yammacin Litini a Maiduguri.

Shima gwamnan jihar Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya mika tasa gaisuwar ga iyalan mamacin.

A takarda da kakakin sa Samuel Aruwan ya fitar yau Litinin El-Rufai ya bayyana cewa da rabon zai gana da marigayin kafin ya rasu.

El-Rufai yace ya ziyace shi a farkon wannan shekara. Yayi addu’ar Allah ya jikan mamacin

Share.

game da Author