An gano wuru-wurun naira bilyan 2.5 a Hukumar Kula da Kafafen Yada Labarai ta Kasa

0

Hukumar ICPC ta tsunduma binciken Hukumar Kula da Kafafen Yada Labarai ta Kasa (NBC), bisa dalilin yin facaka da zunzurutun kudade har naira bilyan 2.5.

An ce an yi facaka da kudaden wadanda aka wawura daga cikin naira bilyan 10 da gwamnatin tarayya ta ware wa hukumar domin aikin maida harkokin tarho zuwa tsari na zamani.

A cikin wata takardar da kakakin ICPC, Rasheedat Okoduwa ta sa wa hannu, ta ce hukumar ta gayyaci Babban Daraktan NBC, Ishaq Kawu ta yi masa tambayoyi.

Ta kara da cewa kuma an gayyaci wasu manyan jami’an hukumar, su ma an ji ta bakin su dangane da yadda aka karkatar da kudaden.

Idan ba a manta ba, cikin 2016, Fadar Shugaban Kasa ta damka wa Ma’aikatar Yada Labarai naira bilyan 10 domin a yi aikin maida layukan tarho zuwa tsari na zamani, wato a Turance daga ‘analogue’ wanda aka gada tun zamanin mulkin Turawa, zuwa ‘digital’ wato na zamani.

An kuma fitar da takardar sharudda cewa wani kamfani mallakar gwamnati ne zai gudanar da aikin.

A kan wadannan sharudda ne sai wasu kamfanoni biyu suka samu amincewar gudanar da aiki. Daya kamfanin mai suna ITS, wani bangare ne daga jikin hakarkarin Gidan Talabijin na NTA.

An damka wa ITS naira bilyan 1.7 a matsayin kudin kafin-alkalamin fara aiki.

Sai dai kuma a jiya Alhamis sai ICPC ta shaida cewa ta bankado akwai badakala da cuwa-cuwa a cikin harkar.

“An gano cewa Kawu ne da kan sa ya yi wuru-wurun mika wa Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed sunan wani kamfani mai suna Pinnacle Communication Limited, wanda aka kamfaci naira bilyan 2.5 aka damka masa.

“An gano kamfanin je-ka-na-yi-ka ne kawai, bai dace a ba shi kwangilar ba.

“An kwashi kudi har naira bilyan 2.5 an zuba a asusun Pinnacle Communications Limited da ke bankin Zenith Bank a cikin watannin Mayu da Yuni, 2017 domin ya gudanar da aiki.

“Shugaban NBC Kawu ya kasa yi wa hukumar NBC cikakken bayanin yadda ya bayar da sunan kamfanin da bai cancanta ba, aka ba shi wadannan makudan kudade.” Haka sanarwar ta bayyana.

An gano cewa shi kan sa Manajan Daraktan kamfanin Pinnacle, Dipo Onifade ya kasa yin cikakken abin da ya yi da kudaden da aka bai wa kamfanin na sa.

ICPC ta kuma gano yadda aka rika karkatar da makudan kudaden ta hanyar da ba su dace ba.

An gano cewa an kwashi naira milyan 100 daga cikin kudin an zuwa a cikin asusun Onifade na Zenith Bank. Amma ya shaida wa matambaya cewa lauyoyi ne aka bai wa kudin masu bai wa Pinnacle shawarwari.
An kuma gano cewa an kwashi naira milyan 400 an zuba a asusun wani kamfani canjin kudaden kasashen waje mai suna Sabdat Investment Limited.

An ce Sabdat ya maida kudaden zuwa dalolin Amurka, kuma ya mika su ga shugaban kamfanin Pinnacle, Lucky Omoluwa, a gidan sa a gidan sa na Kaduna.

Hukumar ICPC ta sha gayyatar Omoluwa cikin girma da arziki ya kai kan sa domin a yi masa tambayoyi, amma ya ki zuwa.

ICPC ta ce saboda tsaurin-ido sai Omoluwa ya garzaya Babbar Kotyn Tarayya, ya nemi ta hana a bincike shi, kuma ta umarci ICPC ta bude masa asusun ajiyar sa da ta kulle a bankin Zenith Bank.

Kotu ta ce tilas Omoluwa ya gurfana a gaban ICPC kafin ranar 3 Ga Disamba, 2018 tukunna kafin ta fara sauraren karar da ya shigar.

Hukumar ta ce Omoluwa ya kai kan sa kuma an ji bayanai masu muhimmanci daga bakin sa, wadanda matambaya suka ce za su yi amfani da su.

Gwamnatin Buhari ce ta nada Kawu shugabancin NBS, wanda shekara uku bayan ya fara aikin, har takarar gwamnan jihar Kwara ya fito a karkashin jam’iyyar APC, aka kayar da shi a zaben fidda-gwani.

Share.

game da Author