Dalilin janyewar Kamfanin General Electric daga aikin gina hanyoyin jiragen kasa a Najeriya

0

Kamfanin General Electric, wanda ya kulla yarjejeniya da Najeriya cewa zai gina titinan jiragen kasa daga Kudancin kasar nan zuwa Arewa, wato General Electric co., ko kuma GE, ya janye yarjejeniya, ya fasa aikin.

Ya bayyana a jiya Alhamis cewa ya tsame hannun sa, amma ya damka shugabancin gina hanyoyin ga wani kamfani na kasar Afrika ta Kudu, mai suna Transnet. Haka kamfanin ya bayyana a jiya Alhamis da dare.

Sanarwar wadda General Electric, kamfanin na kasar Amurka ya fitar, ya ce ya na da yakinin Transnet SOC Limited da sauran kamfanonin hadin gwiwar tare da shi za su iya gudanar da aikin.

Sai dai kuma har yanzu Transnet bai ce komai kan wannan ikirari da aka yin a damka masa aikin ba.

Shi ma kakakin yada labarai na Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, mai suna Ibeleme Israael, ya ki amsa tambayar da PREMIUM TIMES ta yi masa dangane da batun.

Ya ce a dan ba shi mintina kadan zai yi magana, amma har yanzu bai ce komai ba.

Dama kuma a jiya Alhamis da rana, Amaechi ya furta batun janyewar da General electric ya yi daga yarjejeniyar ya yi amfani da kudin sa dala bilyan 2 ya gina hanyoyin jiragen kasa a Najeriya.

Ya yi wannan furucin ne yayin da ya kai ziyara hedikwatar ofishin kamfanin gine-gine na kasar Chana da ke Lagos, wato CCCCC, ya na mai cewa GE ya damka aikin a hannun Transnet SOC Limited.
Amaechi a lokacin ya jaddada cewa aikin ba zai samu tangarda ba.

Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ce ta rattaba yarjejeniyar da GE, wadda gwamnatin APC ta sha yin tinkaho da cewa aikin hanyoyin jiragen kasa din na daga cikin mashahuran ayyukan raya kasa da gwamnatin ta dauko kan yi.

Tun da farko dai Babban Jami’in Kula da Sayen Kayan Aiki na General Electric ne ya shaida wa kamfanin dillancin labarai mafi karfi a duniya, Reuters, a ranar Laraba hakan.

Dama kuma titinan shi kamfanin General Electric din ne zai gina hanyoyin da kudin sa, daga baya kuma ya fanshe kudin sa da ribar sa ta hanyar karbar kudaden sayen tikiti da kudaden dakon kaya masu nauyi da za a rika yi da jiragen na kasa, idan an kammala aikin gina hanyoyin.

A kan wannan yarjejeniya ce da a Turance ake kira ‘concession’, aka amince cewa General Electric zai yi amfani da tsabar kudin sa har dala bilyan 2 ya gina hanyoyin jiragen kasa falan-bib-biyu da za su hade manyan biranen Arewacin kasar nan da na kudanci.

Yarjejeniyar ta amince GE zai gina hanyoyi masu jimillar tsawon kilomita 3,500, daga Lagos zuwa Kano, sannan kuma a gina wasu daga Fatakwal zuwa Maiduguri.

GE shi kuma ya amince zai yi aikin hadin guiwa da wasu kananan kamfanoni irin su Transnet CGETR.UL na Afrika ta Kudu, APM Terminals na Natherland da kuma Sinohydro Consortium na Chana.

Duk da cewa ba a san dalilin yanyewar General Electric daga yarjejeniyar ba, daya daga cikin manyan jami’an Africa Finance Corporation (AFC), wanda shi ne ke kwangilar shigo da kayayyaki, ya shaida cewa ana tattauna yiwuwar shigo da kamfanin Transnet ya maye gurbin GE.

Idan ba a manta ba, cikin watan jiya ne kuma gwamnatin tarayya ta bayyana dakatar da shirin farfado da zirga-zirgar jiragen sama mallakar gwamnatin tarayya, inda aka rada wa kamfanin suna Nigeria Air, tun ma kafin a fara sayo jirgi ko daya.

Daga baya rahotanni sun nuna cewa an dakatar da Nigeria Air, saboda masu zuba jari sun nuna shakku a kan kamfanin na zirga-zirgar jiragen sama din.

Share.

game da Author