Jami’in hukumar kwastam na Najeria Jonah Achema ya bayyana cewa hukumar ta kama kwantena 12 dankare da kwayar Tramadol a tashar jiragen ruwan dake Apapa jihar Legas.
Ashema ya fadi haka ne ranar Alhamis a Abuja inda ya bayyana cewa an kiyasta kudin wannan kwaya zai kai naira miliyan 340.
” Tun a watan Nuwamba 2017 ne muka sami labari cewa za a shigo da wannan kwaya inda daga nan muka fara fakon su har Allah ya bamu sa an kama su.
Discussion about this post