An bankano wani sansani da ake horas da matasa dabarun yaki a boye a Jihar Taraba

0

Shugaban sansanin soji dake aiki a kauyen Serti dake jihar Taraba Sani Adamu ya bayyana cewa sun bankado wani boyayyen wuri da ake horas da matasa dabarun yaki da aka kafa ba tare da sanin jami’an tsaro ko gwamnati ba.

Adamu ya fadi haka ne ranar Alhamis a kauyen Serti dake karamar hukumar Gashaka da yake ganawa da manema labarai.

Ya ce sun gano wannan wuri ne bayan kararrakin da aka yi ta kai musu game da wannan boyayyen wuri wanda mazauna wannan yankin ne suke kai musu karar.

” Muna jin haka sai muka nufi wannan wuri inda muka tabbatar da haka domin mun tadda matasa kusan 300 ana horas da su dabarun yaki a boye.

” Mazauna wannan yanki sun bayyana mana cewa da yiwuwar ‘yan siyasa jihar ne suka kafa wannan wuri domin horas da ‘yan ta’adan da za su yi amfani da su a zaben 2019 idan ya zo.

Bayan haka shugaban karamar hukumar Gashaka Umar Mohammed ya tabbatar wa jami’an tsaro cewa gwamnati ce ta kafa wannan wuri.

Ya ce gwamnati ta kafa sansanin ne domin samar da tsaro a kananan hukumomin Gashaka da Sardauna.

” An zabo mutane 10 daga kowace mazaba dake kananan hukumomin domin su samar da tsaro a yankunan su.

” Sannan mun kuma tattauna da rundunar soja,’yan sanda da SSS domin tanadar wa wadannan matasa da ake horaswa kayan aiki.

Share.

game da Author