An rasa mutane takwas a wani harin da Boko Haram suka kai kusa da sansanin ‘yan gudun hijira a Maiduguri jihar Barno.
Hukumar bada agajin gaggawa na kasa (NEMA) ta sanar wa PREMIUM TIMES inda ta bayyana cewa mutanen da aka rasa a dalilin wannan hari sun hada da yara kanana.
NEMA ta ce Boko Haram sun kai wa sansanin Dalori hari ne da karfe 7 na yamman Laraba sannan sojojin dake sansanin sun yi awowi biyu suna batakashi da Boko Haram kafin Boko Haram suka ci karfin su.
‘‘Boko Haram sun kona gidaje da dama a kauyukan Kofa, Mallumti, Ngomari da Gozari.
Bayan haka wani jami’in rundunar Civilian -JTF mai suna Solomon Adamu ya bayyana cewa gawawwakin mutanen da suka irga bayan wannan hari sun kai 12.
Ya ce Boko Haram sun kashe mutum daya a kauyen Gwazari-Kofa, biyu a sansanin Dalori II sannan mutane tara a kauyen Bulaulin.
Bayanai sun nuna cewa har yanzu mazauna sansanin da kauyukan dake kusa da suka gudu basu dawo ba. Amma wadanda suka sami rauni a dalilin harin na samun kula a asibiti.
Discussion about this post