Tsohon gwamnan jihar Bauchi Isah Yaguda ya canja sheka daga jam’iyyar GNP zuwa jam’iyyar APC.
Tsohon kwamishinan yada labarai na jihar Salisu Barau ne ya sanar da ahaka a garin Bauchi.
Barau ya ce Yuguda ya yanke wannan shawara ne bayan tattaunawa da magoya bayan sa da samun goyon bayan yin haka daga gare su. sannan ya ce yuguda ya canja shekar ne tare da magoya bayan sa har 500,000 da yanzu haka sun riga sun rikide sun zama ‘yan jam’iyyar APC.
Idan ba a manta ba Yuguda fara canja sheka ne tun bayana ya lashe zaben gwamnan jihar a inuwar Jam’iyyar ANPP zuwa jam’iyyar PDP. Hakan yayi sanadiyyar rasa kujerar mataimakin gwamna sa Gyade bayan yaki bin sa zuwa jam’iyyar PDP a wancan lokaci. Bayan ya kammala shekarun sa 8 kan karagar mulki sai ya canja sheka don yayi takarar sanata a jam’iyyar GNP bayan hakan bai yiwu masa ba a PDP.
Yanzu ya canja sheka zuwa jam’iyyar APC.