Zaben Fidda Gwanin Jam’iyyar APC: Gaskiyar Abinda Yake Faruwa A Jahar Zamfara, Daga Imam Murtadha Gusau

0

Bismillahir Rahmanir Rahim

Ya ku Jama’ah! Duk wanda yake nesa ko kuma wanda bai san hakikanin abun da yake faruwa a jahar Zamfara ba game da badakalar da ta kunno kai a kan zaben fitar da Dan takarar fidda gwani na jam’iyya mai ci wato APC, zai yi ta maganganun da basu dace ba, har ta kai ga ya zalunci wasu saboda rashin sani, ko kuma ya rinka hango cewa ko gwamnan jahar wato Abdul’aziz Yari Abubakar yana da gaskiya a kan kumfar baki da tayar da jijiyar wuya da yake yi a kafafen yada labarai. Ko kuma mutumin da ya jahilci me ke faruwa ya dauka cewa bangaren gwamnan ake neman a zalunta saboda babatun da yake yi a kafar yada labarai. Alhali duk wannan ba haka bane, domin gaskiyar magana, tsakani da Allah, shine yake son ya zalunci al’ummar jahar Zamfara, ya danne su, ya hana a basu hakkin su na jefa kuri’a da kundin tsarin mulkin kasar mu Nigeria ya basu, ya kakaba masu Dan takarar da basu so da karfi da yaji.

Imam Murtada Gusau

Imam Murtada Gusau

Jama’ah da farko abinda nike son ku fahimta shine, wallahi, wallahi, wallahi Gwamna shine baya da gaskiya. Dr. Abubakar A. Fari, jami’in da uwar jam’iyya ta kasa ta tura domin ya jagoranci zaben fidda gwani a jahar Zamfara, shine mai gaskiya, kuma wallahi, wannan mutum irin su muke bukata a kasar nan in dai har da gaske ne muna so mu gyara kasar nan.

Hakikanin abun da ya faru shine. Kuma idan nayi karya, Allah ya kama ni, idan na goyi bayan wani daga cikin ‘yan takarar nan, Allah ya hukunta ni da irin hukuncin da ya dace dani. Idan nayi ma wani sharri ko kazafi, sai ya kaini kotu, ko kuma Allah yayi masa sakayya. Dukkanin ‘yan takarar nan su tara, masu neman samun tikitin tsaya wa takarar Gwamna a jam’iyyar APC, a jahar Zamfara wallahi babu wanda ya sanni, ko ya taba ganina. Domin ni bama su ba, babu wani Dan siyasa da zai ce ina zuwa wurin shi neman wani abu. Alhamdulillahi, Allah ya kare ni daga wannan, kuma na gode masa akan haka.

Kawai ni bukata ta shine, in bayyana wa duniya gaskiyar abinda ke faruwa a jaha ta ta Zamfara, domin kubutar da jahar daga rudani da tashin hankalin siyasa da ake neman jefa ta, ba don komai ba, sai don son zuciyar wasu ‘yan tsirarun mutane. Saboda abun da na gani da ido na ya bani tsoro, ya tayar mani da hankali kuma ya gigita ni.

Yau sati daya kenan ina cikin garin Gusau a jahar Zamfara, tun ranar Asabar da ta gaba ta. Kamar yadda kowa ya sani ni Dan Gusau ne, Dan gida ba bako ba.

Tun rana ta farko da hedikwatar jam’iyya ta kasa ta tura wannan bawan Allan Dr. Abubakar A. Fari jahar Zamfara domin yin zaben fidda gwani, Gwamna yace shi bai yarda da shi ba. Meye laifin sa a wurin Gwamna? Laifin sa shine: Domin yace gaskiya za’ayi, domin yaki karbar cin hancin su, domin yaki yarda su saye shi ya zalunci Zamfarawa, domin yaki yarda ma ya tafi wurin su su bashi masauki, sai ya wuce kai tsaye wurin kwamishinan ‘yan sanda. Duk yadda Gwamna zai yi a juya mutumin nan ya zubar da mutuncin sa ya karbi wani abu ayi yadda ake so, bawan Allan nan wallahi yaki yarda. Tsakani na da Allah, wannan shine laifin wannan mutum a wurin Gwamna.

Kuma wannan mutum Dr. Abubakar A. Fari, wallahi ya haihu, kuma ya kai da. Don haka, ya kamata ma mai girma Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sani, irin wadannan mutane sune ainihin abokan aikin sa, da zasu taimaka masa wurin yakar cin hanci da rashawa, ire-iren su ne zasu taimaka masa wurin gyara Nigeria. Domin wannan mutum, wallahi mutum ne mai gaskiya, mai rikon amanah, wanda ba duniya ce a gaban sa ba.

Bangaren Gwamna sun nemi ya basu dukkanin hadin kai domin a danne sauran ‘yan takarar, amma mutumin nan ya kafe, yaki yarda, yace shi gaskiya kawai za’a yi wurin zaben nan.

Laifin shi na farko shine, yaki yarda ya sauka a wurin su su bashi masauki, daga nan su samu damar tattaunawa da shi. Na biyu yaki karbar cin hanci ayi zalunci. Na uku shine sun tura ‘yan ta’addar su wurin zabe, suka kori mutane da duka da sara, da cin mutunci iri-iri, suka yi abinda suke so na son zuciya zalunci, shi kuma ya soke zaben yace sam bai yarda da shi ba. Wallahi kar ka kara kar ka rage, wannan shine laifin wannan jami’i a wurin su. Don haka suke ta kumfar baki su basu yarda da shi ba.

Duk wanda yake cikin jahar Zamfara yasan abun da ya faru ranar laraba da aka yi zaben nan. Gwamnati ta tura ‘yan ta’adda suka afka wa mutane da duka da sara da harbi. Sun ci mutuncin mutane, har da matan aure da tsofaffi da suka fita domin gudanar da wannan zabe.

Wasu sun karye, wasu sun yi rauni mai tsanani, yawanci mutane sun koma gida jina-jina, kai har da rasa rayuka, domin a wannan ranar mutum tara aka kashe a jahar Zamfara, domin kawai gwamnati tana so ta kakaba wa mutane Dan takarar da basu so da karfi da yaji, su kuma mutanen jaha sun ce sam basu yarda ba, sai dai a bar su su zabi wanda suke so.

Gwamnati ta raba kudi da kayan masarufi, domin dai jama’ah su mika wuya, su yarda da Dan takarar da ta kawo, amma duk da haka jama’ah sun ki yarda. Na san wanda ya raba kudin runfuna, nasan wadanda suka raba wa matasa ‘yan ta’adda dari biyar-biyar suka yi abinda suke so, duk abinda ya faru a idon mu aka yi shi.

An watsa ma mata, tsofaffi, da sauran jama’ah tiya-gas domin dai duk a cimma nasarar zalunci, amma duk da haka jama’ar Zamfara dai sun kafe, sun ki yarda.

Don haka ya kamata duniya ta san halin da ake ciki a jahar Zamfara. Duk babatun da Gwamna yake yi a kafar yada labarai wallahi ba gaskiya bane. Sam basu da gaskiya. Suna so ne su kakaba wa mutane Dan takarar da jama’ah basu so da karfi da yaji.

Don haka mutane su sani, uwar jam’iyya, karkashin jagorancin Adams Aliyu Oshiomhole, sune masu gaskiya. Domin su kawai sun ce ne a tsaya tsakani da Allah ayi abunda jama’ah suke so. Shi kuwa Gwamna yace sam ba haka ba, sai dai a bar su suyi son zuciyar da suka ga dama.

Ta yaya za’ayi Gwamna da mukarrabansa duk inda suka shiga cikin jahar Zamfara ake yi masu ihu, ake jifar su, in har suna da gaskiya, kuma jama’ah suna son su? Ni fa wallahi ganau ne ba jiyau ba. Duk abinda ke faruwa a idon mu yake faruwa. Duk inda Gwamna ya shiga, ko wani jami’in gwamnati a Zamfara, wallahi jifar su ake yi ana yi masu ihu. Me ya kawo haka? Saboda Zamfarawa sun ce ba’a taba gwamnatin da suka sha wahalar ta, ta zalunce su kamar wannan ba. Don haka basu son Gwamna da duk wani Dan takara da zai kawo masu.

Wannan abun da nike fada wallahi shine gaskiyar lamari. Kuma ina fadar sa ne tsakanina da Allah, ba tare da shakkar wani mutum ko tsoron sa ba. Allah ne kawai a gaba na.

Kuma ni ban san dalilin da yasa kafafen yada labarai ba zasu ji tsoron Allah su ruwaito ma al’ummah ainihin gaskiyar abinda yake faruwa a jahar Zamfara ba?

Daga karshe ina mai cewa, jama’ah su sani: DAGA CIKIN WADANDA BA’A KARBAR SALLARSU AKWAI:

“Limamin da ya jagoranci Sallah, alhali mutane ba sa son limancinsa.” [Imamu Tirmizi ne ya ruwaito kuma ya inganta shi]

Wannan a limancin Sallah kenan fa, TO INA GA JAGORANTAR AL’UMMAR JIHA KO KASA BAKI DAYA!!!

Don haka Musulunci addini ne mai kimantawa da darajjanta zabin mutane, don haka shuwagabanni da masu ruwa da tsaki a zabe, su ji tsoron Allah, su zabawa al’umma shuwagabannin da suke da ra’ayi da su, kuma suke son su. Idan ba haka ba kuwa, zaman lafiya zai yi wuya a cikin al’ummah. Allah ya sawwake kuma Allah yasa mu dace, amin.

Dan uwanku:

Imam Murtadha Muhammad Gusau. Za’a iya tuntubar sa a wannan adireshi kamar haka: gusaumurtada@gmail.com ko kuma +2348038289761.

Share.

game da Author