TATTAUNAWA: Ni ne dan takarar PDP da zai iya kada Buhari a zaben 2019 – Kwankwaso

0

Daya daga cikin ‘yan kakarar shugaban kasa a Inuwar jam’iyyar PDP, kuma sanatan da ke wakiltar Kano a majalisar dattawa, Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa, ko tantama baya da shi cewa idan har jam’iyyar sa ta PDP ta tsayar da shi dan takarar shugaban kasa zai kada Buhari a zaben 2019.

Kwankwaso ya jaddada haka ne a hira da yayi da wakilan PREMIUM TIMES, Mojeed Musikilu da Festus Owete a Abuja.

Bayan nan ya lissafo irin shirye-shiryen da ya yi wa kasa Najeriya idan har ya dace da zama shugaban kasa.

PT: Kana daya daga cikin ‘yan takara 12 dake neman jam’iyyar PDP ta tsayar dan takarar ta na shugaban kasa, Me ya sa kake ganin kai ne kafi dacewa jam’iyyar PDP ta tsayar dan takarra ta?

Kwankwaso: Tabbas ko haufi bani da shi cewa idan na dace da cin zaben fidda gwani zan kada Buhari. Nine kadai dan takaran da ke da magoya baya a ko ina a Arewacin kasar nan. Babu gidan da zaka shiga baka samu mutum daya da yake yin Kwankwasiyya ba.

Za ka ga ko dai direba, ko mai dafa abinci, ko dan gida ko yaron gida dan Kwankwasiyya.

Na yi aikin gwamnati, na zama mataimakin kakakin majalisar Tarayya, na yi ministan tsaro a kasar. Na samu kwarewa sannan tabbas dandazon magoya baya na za su yi tasiri matuka a zaben 2019 wanda ba sai mutum ya jira PDP ta yi masa komai ba.

PT: Kana ganin da wadannan hujjoji da ka jero zaka iya yin tasiri?

Kwankwaso: Kai shi ma da kan sa shugaban kasa ya sani cewa idan na samu tikitin takara zan kada shi a zabe.

Idan har na samu wannan tikiti, ita kan ta PDP ta sani cewa mai-gama ya-gama lashe zabe zai tabbata. Mulki za ta dawo hannun PDP ko shakka babu.

Daga nan sai mu dawo mu hada kan kasa Najeriya, a kawo karshen kashe-kashen da ake yi a kasar nan sannan a seta kasar yadda za ta dawo kan hanya mikakkiya.

PT: Da irin wannan kuranta kai da ka ke yi, yaya ba ka tattauna da jam’iyyar ka su ba ka tikiti kawai ba sai an yi zaben fidda gwani ba.

Kwankwaso: Ba a haka a siyasa, duk dan takara sai da ya siya fom, naira miliyan 12. Ka ga ko ba zai yiwu mutum ya ce a bari ba.

Idan a ka yi zaben, kowa zai fi yadda da jam’iyyar sannan mutane kuma za su yarda da mu.

PT: Ka ce a ko wani gida akwai dan kwankwasiyya a Arewa, a Kudu fa?

Kwankwaso: Ko a kudun ma muna da magoya baya masu yawa. A jihar Edo akwai ‘Yan Kwankwasiyya sama da mutane 500,000 sannan a jihar Ribas akwai sama da ‘yan Kwankwasiyya 270,000. Sannan akwai su da dama a wasu jihohin.

PT: A yanzu dai kana cewa kenan kafi Buhari yawan masoya a Kano kenan ?

Kwankwaso: Kwarai da gaske, ai hakan ba boyayye bane. Kowa ya sani kuma ya gani.

PT: Amma ance masu son Buhari makafi ne. Idan ba shi ba basu ganin kowa. Me za kace kan haka?

Kwankwaso: Yanzu fa kowa yunwa ya sa idon sa ya bude wasai. Kowa ya gane gaskiya ya san inda muka dosa.

PT: Shin ko wani daga cikin sauran ‘yan takara ya tuntube ka fon ka janye masa. Domin mun ji Atiku tattauna da wasu?

Kwankwaso: Babu wani da yayi haka, irin haka da kamar wuya fa. Sai dai na sani cewa a Fatakol za a samu irin haka, tabbas. Akwai yiwuwar wasu su janye wa wasu idan aka samu daidaituwa.

PT: Kana ganin za ka iya janye wa wani dan takara?

Kwankwaso: Eh mana Idan har akwai wanda yafi ni cancanta, zan janye mana, amma fa sai idan ya fi ni cancanta.

PT: Toh, ai ya kamata ace ka fi mu sani ko akwai.

Kwankwaso: A’a, idan dai akwai za ayi abin da ya dace.

Share.

game da Author