Buhari ya nemi Majalisa ta amince masa kara ciwo bashin dala bilyan 2.78

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya aika wa Majalisar Tarayya kokon barar neman amince masa kara ciwo bashin dala biliyan 2.78 domin biyan somin-tabin fara wasu ayyukan da ke cikin kasafin kudi na 2018.

Wannan wasika da Buhari ya aika wa Majalisa tun a ranar 23 Ga Yuli, jiya ne Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya karanta ta a zauren majalisar dattawa, jim kadan bayan fara zaman ta bayan dawowa daga hutun da majalisar ta tafi tun ranar 25 Ga Yuli.

Buhari ya ce ya na son sake ciwo bashin ne daga manyan kamfanoni da cibiyoyin hada-hadar kudade ta duniya, domin cike gibin da aka samu na kudade a kasafin 2018 tare kuma da yin aiki da su a wasu ayyukan inganta ci gaban kasa da ke cikin kasafin 2018 din.

Ya ce bashin na yarjejeniyar tsarin lamuni na ‘Eurobonds’ ne da kuma wasu hanyoyin tasarifin kayyadaddun yarjejeniyar kudade a manyan kasuwannin duniya.

Har ila yau, a cikin wasikar, Buhari ya nemi a kara masa wata dama ta kara lalubo wasu dala milyan 82.54 domin sake cike gibin dala milyan 500 ta daban da aka samu daga tsarin ‘Eurobonds’.

Buhari ya ce ya yi haka ne a bisa yadda ka’idar da dokar Hukumar Kula da Basussuka ta Kasa ta gindaya, kuma dokar ce dama ta kafa hukumar, a cikin 2003.

Share.

game da Author