Jihar Gombe ta rasa yara 310 a shekaru biyu da suka wuce

0

Wani ma’aikacin kiwon lafiya a jihar Gombe Suleiman Mamman ya bayyana cewa jihar Gombe ta rasa yara 310 a tsakanin shekaru biyu.

Ya fadi haka ne da yake ganawa da PREMIUM TIMES a garin Gombe.

Mamman ya bayyana cewa wadannan yara sun rasu ne a dalilin yunwa da kamuwa da cututtuka da suka yi. An rasa yaran ne a asibitocin dake kananan hukumomin Gombe, Dukku, Nafada da Kaltungo.

Ya ce a shekarar 2016 an kawo yara 12,618 asibitocin jihar daga cikinsu 11,531 sun warke, 105 sun mutu, 833 iyayen su suka tafi dasu kafin su sami sauki sannan 149 basu samu sauki ba.

A shekaran 2017 an kawo yara 14,143 asibitocin jihar inda 105 daga ciki suka rasu, 13,069 suka warke, 710 iyayen su suka dauke su sannan 214 basu warke baa lokacin.

A 2018 kuwa an kawo yara 10,171 asibitocin jihar inda daga ciki 6906 suka warke, iyayen 385, sukatafi dasu, 2664 na samun kula, 55 suka mutu sannan 81 ba su warke ba.

Mamman ya ce bincike ya nuna cewa kamuwa da cututtuka kamar su kanjamau na daga cikin matsalolin da ya hana wadannan yara warkewa sannan yace sun aika su manyan asibitocin dake jihar domin samuna ci gaba da duba su.

” Jihar Gombe na cikin jihohi 12 a Najeriya dake fama da matsanancin mace-macen yara kanana a dalilin yunwa domin bincike ya nuna cewa yara 361,000 ake rasawa a jihar duk shekara.”

Share.

game da Author