Kungiyar Manoman Shinkafa Reshen Jihar Katsina (RIFAN), ta roki ‘yan kungiyar da su ka ci gajiyar bashin kudaden noman shinkafa da su gaggauta biya.
An bayar da bashin ne a karkashin tsarin nan na ‘Anchor Borrowers Programme (AB).
Shugaban kungiyar RIFAN, ta manoman shinkafar jihar, Shuaibu Wakili ne ya yi wannan kira a lolkacin da ya ke zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, a Daura, ranar Talatar da ta gabata.
NAN ya ruwaito cewa akalla an bai wa manoma 56,000 bashin kudade domin su noma shinkafa a lokacin ranin shekarar da ta gabata, ta 2017, a cikin kananan hukumomi 36 da ke fadin jihar.
Wakili ya tunatar da wadanda suka karbi bashin cewa shekara daya ce aka rattaba alkawarin cewa kowa zai biya bashin da ya karba ta hannun shugaban kungiya na karamar hukumar da manomin ya ke.
“Ana jiran kowanen mu ya biya bashin da aka ba shi da buhunnan shinkafa 10 a kowace hekta daya da ya noma shinkafa a cikin ta.”
Daga nan sai ya roki manoman da su gaggauta biyan bashin bara, domin tuni an fara tsarin sake bada wani lamunin a wannan shekarar ta 2018.
Ya sha alwashin cewa za su kara yawan mambobin kungiyar yadda za su kai 80, 000 domin karin yawan wadanda za su ci gajiyar tsarin.