Kira ga matasa masu jiran aikin gwamnati a Najeriya, Daga Mustapha Soron Dinki

0

Ina yiwa matasan Najeriya fatan alheri a duk inda suke. Tabbas kowa da hanyar da ya zaba a rayuwa musamman akan abunda ya shafi aikin yi. Sai dai mafi girman kalubale shine rayuwar matashin da ya gama karatu ya dogara da gwaunati ta bashi aiki.

Babu shakka duk wanda ya gama karatu a Najeriya musamman a garuruwan da basu da kasuwanni burinsa ya samu aikin gwamnati shiyasa fiye da kaso sittin na wadannan matasa suna shan wahala a kasuwar aiki (Labour market) musamman ‘ya’yan talakawa wadanda ko darakta guda daya basu dashi a cikin zuri’ar su.

Malam bahaushe yace “Ba’a cizon mu’umini sau biyu a rami daya.” Dole sai ya samarwa da kansa rigakafi in dai yana da hankali. Gwamnati ba zata iya bawa matasan Najeriya aiki ba musamman irin tamu da take fama da rikici iri iri.

Shekara da shekaru matasan kasarmu suke fuskantar cikas da tasgaro bayan sun gama karatu shiyasa mafi yawancinsu suna cikin fatara da talauci. Kusan komai na wadannan matasa yana zuwa ne a makare.Yana da wahala ka samu mutum a cikin nutsuwa a qasa da shekara Arba’in da biyar saboda yanayi na rashin samun komai akan lokaci.

Mafita itace,ya kamata ko wani matashi ya samawa kansa mafita tun kafin ya gama makaranta. Gaskiya yanzu ya zama tsohon tunani ace baka da aikin yi. Duk duniya babu wanda ya fika son cigaban ka.

Menene amfanin Diploma ko NCE ko degree ko masters ko ph,D idan ba zata samar maka da hanyar da zaka rayu ba? Gaskiya a irin kasashenmu ne ake gama karatu kuma a jira gwamnati ta bada aiki.

Misali, wanda ya karanta engineering ko law ko medicine ai bashi da bukatar ya 6ata shekara biyar yana jiran aikin gwamnati. Haka zalika ko me ka karanta a makaranta zai iya baka aikin yi saidai zuciyar ka ce take da rauni.

Babu maraya sai rago, kuma duk wanda ya dogara da wani a duniya ya shiga uku.Gwara ka qirqirowa kanka abun yi kafin kayi tunanin wani ya taimakeka. Su wadanda kake sa rai zasu baka aiki, wallahi ba zasu baka ba saboda dalilan da ba sai na fada ba. Akwai wanda ko direbansa ba zai daukeka ba saboda kada ka rabashi, wani ma zai so ace ya rabaka da certificate din don kada ka kamo ‘ya’yan sa a lokacin da shi yayi ritaya ko ya mutu.

Kowa ya auna wannan maganar tawa,don haka matasa ku yi tunani akan makomar rayuwarku.Ni Soron-dinki kimiyar siyasa na karanta amma shaida ta rage a hannunku idan kwalliya nake yi da ‘dan qaramin karatun da nake dashi.

Duk mutumin da ya karanta Mass comm ko English yana da damar qirqirarwa kansa sana’a,kaima haka wanda ka karanta Hausa da sauransu. Kowa yaje ya rufe kansa a daki yayi tunanin abunda zai iya yi.Mafi qarancin abunda zaka fara yi shine siyar da iliminka saboda ilimi haja ce da ake siyar da ita.Ka kula ko “lift” kake nema akan hanya an fi taimaka maka idan aka sameka ka fara tafiya,ba wai ka tsaya kamar bishiya kana sakawa mutane hannu ba.

Allah yasa mu ga Alheri.

Share.

game da Author