Manyan kungiyoyin sa-kai da suka sa-ido don ganin yadda zabe ke gudana a jihar Osun, sun bayyana zaben raba-gardama da aka gudanar yau Alhamis a wasu sassa na jihar Osun, cewa an tafka cuwa-cuwa, harkalla, kuma ya raba hanya da duk wani tafarkin dimokradiyya karbabbe.
Kungiyar CCD ta yi tir da zaben tare kuma da yin kira da a binciki hukumomin gwamnati masu hannu a cikin zaben.
Wadanda aka fi yin tir da Allah-wadai da halin da suka nuna, su ne jami’an ‘yan sanda, wadanda CCD ta ce su ne ya kamata su nuna halin dattakon kishin dimokradiyya.
“A iya sa-idon da muka yi domin ganin ko an bi tsarin da doka da kuma dimokradiyya ta shimfida a zaben raba-gardamar da aka yi a yau Alhamis, 27 Ga Satumba, 2018, mun hakkake cewa wannan zaben bai kai ko da wata alamar da ke nuna cewa an yi adalci ba.
“Don haka mu na jaddada cewa zaben harigido ne kawai aka yi, amma ba zabe ne wanda dimokradiyya za ta amince da shi ba.”
Daraktan CCD, Idayat Hassan, ta ce kungiyar ta ta lura da cewa jami’an tsaro sun yi harkalla da murdiya sosai a wurin zaben, har ma ta kai su ga muzguna wa ‘yan jarida, masu sa-ido da kuma ‘yan jam’iyyar adawa.
“Jami’an tsaro sun rika tozarta ma’aikatan kungiyar mu, har ta kai su ga kama wasu su na tsarewa, musamman a karamar hukumar Orolu, alhali kuma su na da cikakkar shaidar cancantar zuwa aikin sa-ido a wurin zaben.” Inji CCD.
“CDD ta kuma lura da cewa akwai zaman dar-dar a Ifon, cikin karamar hukumar Orolu, sakamakon wuce makadi da rawa da jami’an tsaro su ka rika yi, wadanda suka rika taimaka wa wani bangaren siyasa baya.”
CCD ta ci gaba da kawo hujjoji da bayanan da ta ce sun taimaka wajen munantawa da muzanta zaben, tare da hujjojin yadda aka tafka magudi, musamman ta yin amfani da jami’an tsaro.