Ba da sani na aka tsare Sani Baba-Inna ba- Aisha Buhari

0

A yau Alhamis ne uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta bayyana cewa ba da sanin ta aka tsare mai tsaron ta ba wato ADC Sani Baba-Inna wanda jami’an tsaro suka yi.

Aisha ta fadi haka ne a wata takarda da ya fito daga ofishin ta wanda mai taimaka mata kan yada labarai Suleiman Haruna ya saka wa hannu.

Aisha ta zargi Sani wanda ya fara aiki da ita a 2016 da laifin amfani da sunan ta wajen karban kyaututtuka wajen mutane.

Ta ce tana da masaniya game da munanan aiyukkan Sani amma kama shi da jami’an tsaro suka yi ne ba ta sani ba.

Daga nan Aisha ta kuma tabbatar da cewa ita ko ‘ya’yan ta basu taba aika wani ma’aikaci ya karbo musu alfarma ta kowacce iri daga hannun wani ba.

Share.

game da Author