Har gara wasan kwaikwayo da zaben raba-gardamar Osun – Adeleke

0

Dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamnan Jihar Osun, Nuruddeen Adeleke, ya bayyana cewa har gara ma wasan kwaikwayo zai iya cewa ya fi zaben raba-gardamar da aka gudanar yau a wasu sassan jihar Osun.

Adeleke ya tsine wa zaben tare da yi masa tofin-Allah tsine, ya na mai cewa ko mahaukaci ba zai yarda da wannan sakamakon zabe ba.

Dan takarar ya bayyana matsayin sa ta hannun ofishin yakin neman zaben sa, ganin yadda aka rika samun rahotannin tsorata masu jefa kuri’a a wasu sassa da kuma wasu tashe-tashen hankula a wuraren zabe, musamman ma a Karamar Hukumar Orolu.

“Duniya gaba daya ta shaida sakarcin da aka yi a jihar Osun, wai shi zabe. An dai yi amfani da karfin jami’an tsaro da kuma karfin gwamnati an danne wa mutane abin da ran su da ra’ayin su ya fi kawai.

“ Shi kan sa ma zaben raba-gardamar da aka sake gudanarwa a yau, bai ma taso ba kwata-kwata.

Daga cikin wadanda suka bada rahoton tayar da hankula a wuraren zabe, akwai ‘yan jarida, masu sa-ido da kuma masu zaben da aka zaton ‘yan PDP ne. Dukkan su sun nuna rashin jin dadin ‘yadda wasu ‘yan ta-kife da aka tabbatar na APC ne suka hargitsa zabe, musamman a Karamar Hukumar Oroli.

A zaben yau Alhamis ma an kama wakilin wannan jarida a karamar hukumar Oroli, don ya dauki hotunan yadda zaben ke gudana, amma jim kadan ‘yan sanda suka sake shi.

Share.

game da Author