Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA), ta bayyana cewa sama da rayuka 100 ne suka salwanta sakamakon ruwan sama mai karfin gaske da aka rika shekawa wanda ya yi sanadiyyar cika da tumbatsar Kogunan Neja da Benuwai.
Cika da tumbatsar da wannan koguna suka yi ne ya sa suka rika yin ambaliya su na cin rayuka da kananan kauyukan mazauna gefen tekunan guda biyu, tara da yin asarar dukiyoyi masu bimbin yawa.
Ganin Haka ne NEMA ta kafa dokar-ta-bacin yaki da ambaliya a jihohin Kogi, Neja, Anambra da kuma Benuwai da Delta.
Hukumar ta bayyana cewa a zaman yanzu kuma jami’an ta na sa-ido sosai domin kauce wa aukuwar irin haka ko kuma rage barnar ambaliyar da daukar matakan gaggawa a jihohin Taraba, Adamawa, Kebbi, Edo, Rivers, Benuwai, Bayelsa da Kwara.
Kakakin NEMA Sani Datti ne ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ambaliya ta ci rayuka sama da 100, ya na mai karawa da cewa jihohi hudu na cikin mummunan hali da yanayi.
A duk shekara daruruwan jama’a na mutuwa a Najeriya sanadiyyyar ambaliya, tare da asarar dubban gidaje da bimbin dukiya.
A wannan shekara babu takamaimen adadin mutane da suka mutu sanadiyya ambaliya, amma dai Gidan Radiyon BBC ya ruwaito cewa mutane 40 sun mutu a jihar Neja kadai.
Kafin nan kuma Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar da rasuwar mutane 31 a jihar tare da asarar gidaje sama da 10,00 a cikin kananan hukumomi 15 daga kananan hukumomi 44 da ke jihar.
A jihar Katsina an yi asarar sama da mutane 50 bayan da Kogin Jibiya ya yi ambaliya cikin garin sakamakon wani ruwa kamar da bakin kwarya da aka rika shekawa da dare a farkon watan Agusta.
A lokacin da Gwamnan Jihar Katsiana Aminu Masari ya kai ziyara garin Jibiya, kwana daya bayan ambaliya, ya bayyana alhinin sa da cewa:
“Ni dai da ido na ban taba ganin irin wannan mummunan bala’i ba.” Inji Masari a cikin jimami.
“Tsawon tashin ruwan sama da ya yi toroko, ya kai kafa goma. Sai dai mu ce wannan annoba ce daga Allah kawai, domin duk mun gina magudanan ruwa da kai kwararar da ruwa a cikin Kogin Jibiya.
“Amma ruwan da ke malalawa cikin kogin ne ya rika dawowa da baya zuwa cikin gari.
“Na ga matashi ango sabon aure, kwana uku da daura aure, ya na ta fagamniyar neman amaryar sa. Abin ban-tausayi.
Tuni dai Masari ya ce an maida wadanda suka rasa matsugunan su zuwa firamare ta garin, kuma NEMA ta kai agajin gaggawa na kayan abinci da sauransu, har cikin mota 13.
Ya kuma yi kira ga Ma’aikatar Muhalli da a karkatar da ruwan, ta yadda zai daina kwarara a cikin kogin.
Babban Sakataren Hukumar Agajin Gaggawa ta jihar Kano, Ali Bashir, ya kiyasta barnar da mabaliya ta yi a jihar Kano cewa ta kai naira bilyan biyar.
A ranar Juma’a da ta gabata kuma, ofishin NEMA na Arewa-maso-yamma, ya bayyana cewa a jihohin Katsiana da Kaduna ambaliya ta ci rayuka 100.
Kodinatan NEMA na wannan shiyya, Isa Chonoko ne ya bada wannan adadin a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN.
Ya ce mutane 51 suka mutu a jihar Katsina, 30 suka bace har yau babu labari a Jibiya, duk a jihar Katsina.
Shugaban Hukumar NEMA Sani Datti dai ya ce tuni Gwamnatin Tarayya ta baiwa hukumar ta sa naira bilyan 3 domi a shawo kan barnar ambaliya a fadin kasar nan.
Ko a jiya Litinin sai da Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello ya kai ziyara ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, inda ya bayyana masa irinn ta’adin da ambaliya ta yi a jihar sa.
GARGADIN NEMA KAN AMBALIYA
Makonni biyu da suka gabata ne dai Hukumar Agajin Gaggawa ta Kasa NEMA, ta gargadi jihohi da kananan hukumomi da su gaggauta yin kwakwaran shiri domin kauce wa ambaliya a yankunan su.
Jagoran da Gwamnatin Tarayya ta nada ya shugabanci kwamitin wayar da kai ga jama’a ne ya bayyana haka a wani taro da aka gudanar a Fatakwal.
Umar Mohammed ya ce makasudin wannan taro shi ne a tsara wa masu ruwa da tsarin da suka halarci taron shirin gaggawa da ya dace kuma ya wajaba a dauka idan har akwai alamun barkewar ambaliya a yankunan su.
Ya roki sauran jama’a su shiga cikin wannan gagarimin aikin wayar da kai da kuma daukar matakan kauce wa barkewar ambaliya.
“Wajibin gwamnatocin jihohi ne su tanadi wuraren fakewa da kuma matsugunai ga wadanda ambaliya ta yi wa barna, domin ita dai ambaliya abu ne da ba mu iya tsayar da ita. Amma fa a mu na iya rage ta, ta hanyar daina toshe magudanun ruwa da manyan hanyoyin da ruwa ke bi ya na wucewa, kwalbatoci da kuma daina yin gine-gine a kan hanyar da ruwa ke wucewa.”
“Jihohi da kananan hukumomi su rika bai wa jami’an NEMA hadin kai ta hanyar gaggauta amsa kiran su idan batu na daukin gaggawa ya taso.”
“A shirye mu ke mu gaggauta zuwa cikin hanzari a duk lokacin da kowace jiha ta kira mu, don haka mu na yin kira ga jihohi da su tanadi wuraren fakewa ga jama’a idan hakan ta taso a cikin gaggawa.
FARGABAR KWARAROWAR RUWA DAGA KAMARU
Cikin makon da ya gabata, al’ummar da ke zaune a gefen Kogin Benuwai sun shiga cikin halin fargaba, bayan da aka rika yada labarin cewa Madatsar Ruwa ta Lagbo ce kasar Kamaru ta balle, shi ya sa ambaiya ta mamaye wasu yankunan.
An ci gaba da yada cewa kowa ya tsere daga yankin, domin Kamaru za ta sake balo ruwan ya kwararo cikin Najeriya.
To sai dai kuma Shugaban Riko na Hukumar Kula da Sauyin Yanayin Damina, NIHSA, Ahmed Mabudi, ya bayyana cewa ji-ta-ji-ta ce kawai da wasu ke yadawa wai yawan ambaliyar da ake samu a Najeriya, ya na faruwa ne sakamakon balle dam din Lagbo da kasar Kamaru ta yi.
Kamfanin Dillancin Labarai, NAN ya ruwaito ji-ta-ji-tar da fargaban da ake yadawa cewa mutanen da ke zaune a gefen Kogin Neja da na Benue su tashi kowa ya tsere, domin Kamaru ta saki ruwan Lagbo Dam da ke kwarara a cikin Najeriya.
Amma Mabudi ya ce wannan gana karya ce kawai ba gaskiya ba ce. Kuma mutane su guji tada hankalin jama’a.
“Mun yi magana da babban jami’an da ke kula da Madatasr Ruwa ta Lagbo, mai suna Abdullahi da ke cikin Kudancin Kamaru. Kuma dama a kullum mu na tuntubar sa.
“Kuma dama akwai rubutacciyar yarjejeniya tsakanin Najeriya da Kamaru cewa ta ba Majeriya isasshen lokacin da za ta yi shiri tare yin kaye-kaye da daukar matakai a duk lokacin da za ta saki ruwan na Madatsar Lagbo.”

“A ranar Talata mun yi magana da Abdullahi, kuma ya shaida mana cewa a yanzu ruwan ya kai ma’aunin 12.1m, kuma sai ya kai 12.6 sannan za ta balle shi domin ya kwarare.
‘Tabbas mun san ruwa ya karu a Kogin Adamawa, Taraba da Benuwai. Amma da mu ka tuntubi Abdullahi ko sun saki ruwa, sai abin ya ba shi mamaki. Ya ce yawan da ruwan ya yi sai dai ko sakamakon irin karfin da ruwan saman da ake yawan yi ne yanzu ya yi sosai.
NAN ta ruaito kuma a ranar Asabar cewa karfin yawan ruwan Lokoja ya haura 11.m.
Idan za a iya tunawa, a duk shekara Kamaru na balle ruwan ‘Lagbo Dam’, inda ruwan kan kwararo cikin manyan koramu da kogunan Najeriya, musamman a Adamawa, Taraba da Benuwai.
Kamaru kan yi haka ne sanoda idan madatsar ruwar ta ta cika, to zai yi ambalia a cikin kasar.