Kotu dake Ibadan ta gurfanar da wani malamin jami’ar koyar da aiyukkan noma dake Ibadan mai suna Aremu Olufemi da laifin kwana da daliban sa maza ta baya.
Lauyan da ya shigar da karan Mathew Ojeah ya bayyana cewa Olufemi mazaunin layin Olugbode ne a unguwar Odo-Ona a garin Ibadan sannan yakan nemi dole ya kwana da daliban sa ne ta hanyar kada su a jarabawa.
” Idan daliban na sa sun zo neman samun bayanin yadda suka fadi sai Olufemi ya bukaci sabuwar wayar tarho mai suna Infinix Hot note IV daga wurin su.
Ojeah yace a lokacin da dalibi zai kawo masa wayar da ya bukata ne sai ya nemi kwana da su.
Ya kuma kara da cewa wannan bashi bane karo na farko ba da Olufemi ke aikata irin wannan ta’asa
domin kuwa akwai wani dalibi mai suna Jamiu Lateef.
Yayin da yake kare kan sa Olufemi ya musanta aikata haka a kotun sannan lauyan dake kare shi J.A. Apo ya nemi kotu da ta bada belin Olufemi.
A karshe alkalin kotun Jejelola Ogunbona ya bada belin Olufemi kan Naira 50,000 tare da gabatar da shaida guda daya.
Za a ci gaba da shari’ar ranar 19 ga watan Oktoba.
Discussion about this post