Yayin da zaben 2019 ke bijirowa a farkon sabuwar shekara mai zuwa, an bai wa alkalan Najeriya umarnin cewa su tabbatar da gaskiya da gudanar da shari’u ba tare da yi wa wasu kararrakin zabe hukuncin ‘gaba-gadii’ ba.
Alkalin Alkalan Babbar Kotun Tarayya, Adamu Kafarati ya bayar da wannan umarni a jiya Litinin, inda ya umarci dukkan alkali su daina yanke hukuncin jingine wata shari’ar da aka fara, ko wadda ba a kai ga faraway ba. A Turance dai ana kiran wannan hukunci da suna ‘ex-parte motion’.
ME AKE NUFI DA ‘EXPARTE MOTION’?
‘Exparte Motion’ ko Hukuncin Rataye Shari’a, wani baubawan burmin kwarya-kwaryan hukuncin gaba-gadi ne da mai shari’a kan yanke, ta hanyar dakatar da wata kara da aka shigar, ko da an fara sauraren ta, ko kuma ba a fara sauraren ta ba.
Amma akasari alkali na yanke hukuncin ne kafin nya fara sauraren kowane bangare na mai shigar da kara ko kuma wanda aka kai kara.
YA ‘EXPARTE MOTION’ YA KE?
Wannan baubawan burmin hukunci dai an fi yin sa ga ‘yan siyasa, wadanda mafi yawan shari’u ko kararrakin su duk wadanda suka jibinci siyasa ne, ko kuma wani laifn da suka aikata lokacin da suke kan mulki.
Yadda ‘ex-parte motion’ ya ke shi ne, idan wani dan siyasa ko hukumar cin hanci da rashawa, EFCC ko ICPC su ka maka wani dan siyasa kotu, maimakon ya je ya kare kan sa daga hukunci, tuhuma ko cajin da ake yi masa, sai kawai ya zarce wata kotun ya shigar da kara cewa, ya na rokon kotu ta hana waccan kotun binciken karar sa da wani ko wata ko kuma wata hukumar ta kai shi.
Shi kuma wannan alkali, sai ya tashi ba tare da sauraren bangarorin biyu domin ya ji dalilin da zai sa ya rataye karar bisa maratayi, ko a kan igiya ba, sai kawai ya yanke hukuncin cewa ai waccan kotun ba ta da hurumi ko karfin iko ko cancantar sauraren waccan karar.
Sau da yawa saboda irin wannan hukuncin ‘gaba’gad’i da alkalai kan yanke nan take, su kan jawo dadewar shari’u su dauki shekara da shekaru ba a kammala ba.
Ana kai irin wannan kara ce a kotun da ke sama da wadda aka kai mutum kara.
Da ya ke bayyana dalilin daukar wannan mataki, Kafarati ya ce an yi haka ne domin a magance tarnaki da dabaibayin da ake samu a kotunan kasar nan a shari’u na manyan ‘yan siyasa.
Kadan daga cikin irin wannan kararraki na kurman hukunci da ke gaban kotu sun hada wanda Sanata Isa Misau da Sanata Rabfi’u Adebayo suka shigar, inda suka nemi kotun tarayya ta hana shirin tsige Saraki a cikin watan Yuli, bayan ya fice daga jam’iyyar APC zuwa PDP.
Akwai kuma wata kara da Sanata Ovi Omo-Agege ya shigar da majalisar tarayya, inda ya nemi kotu ta haramta dakatar da shi da majalisa ta yi.
A Najeriya akwai irin wadannan da dama.
Shekaru 12 kenan ana buga kwatagwamgwamar shari’ar tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu, daga wannan kotu ana tuma tsalle zuwa wata kotun. Har yau babu shekara, wata, mako, rana ko lokacin karewa. domin a yau ma ta na daga cikin shari’un da aka jingine, aka ce sai cikin 2019 za a ci gaba da su.
Discussion about this post